RASHIN TSARO: Hukumar Zabe ta dage zabe a karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara

0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Zamfara (INEC) ta dage zaben gwamna da majalisar dokoki na jihar a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi.

Garba Galadima ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Lahadi inda ya kara da cewa hukumar ta yanke wannan haka ne saboda rashin tsaron da ake fama da shi a wadannan kananan hukumomi.

Galadima ya kara da cewa zabe ya gudana a wasu sassan jihar sannan har zuwa yanzu tantance sakamakon zaben da aka riga aka yi a jihar domin bayyana su.

Share.

game da Author