An kashe akalla mutane 113 a Jihar Zamfara a cikin mako daya, tunn bayan bayyana sakamakon zaben da aka sanar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara.
An tabbatar da mahara masu kashe mutane da yin garkuwa da su, sun kuma lalata gidaje da kona dukiyoyi za su kai na milyoyin nairori.
Biyo bayan wannan kisan-bagatatan ya sa mazauna kauyukan yankin Shinkafi, Anka da Tsafe sun gudu daga garuruwan su zuwa cikin sansanonin masu gudun hijira.
Ranar Asabar da ta gabata, ‘yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da kashe mutane 29 a Karamar Hukumar Shinkafi kadai.
An kuma kashe wasu mutane 30 a kauyen Kware, wanda PREMIUM TIMES Hausa ta bayar labarin kisan da a ka yi musu tun farkn wannan watan.
Wani mazaunin yankin mai suna Bala Shinkafi, ya ce mahara suna tafiya ne a cikin jerin gwanon babura kowane kuma dauke da goyon dan bindiga daya, kimanin su su 100.
Ranar Lahadi da ta gabata kuma mahara sun kashe mutane 20 a kauyen Danjibga.
Ya ce mazauna Keta da Kwaren Ganuwa da suka hada ‘yan kato da gora domin su kori ‘yan ta’addan, fadan ya karke ga rasa rayukan kato da gora har mutum 20.
A daidai wannan lokacin ne kuma aka kashe mutane 14 a kauyen Kaware da ke cikin Karamar Hukumar Anka.
Har ila yau rahoton yace sun sace mutane 60, cikin har da wani dagacin gunduma daya.
Kakakin Operation Sharan Daji, Clement Abiade ya tabbatar wa jaridar Thisday kisan mutanen, amma bai fadi adadi ba.
A halin yanzu dai jama’a sai kauracewa suke yi daga kauyukan da abin ya shafa, har ma da wadanda bai shafa ba.
Discussion about this post