Rundunar ‘yan sandan FCT Abuja ta hana jama’a da masu ababen hawa zirga zirga a Abuja da garuruwan da ke kwayen ta.
Kakakin rundunar, Anjuguri Mamzah ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya fitar ga manema labarai yau Alhamis.
Mamzah ya ce an hana zirga-zirga daga karfe 6 nasafe zuwa karfe 6 na yamma.
Ya ce amma an sahale wa motocin daukar marasa lafiya na asibitoci, motocin Hukumar Kashe gobara da wasu masu gudanar da ayyuka na musamman cewa dokar ba ta shafe su ba.
Ya bai wa jama’a hakurin takurar da jama’a za su yi, sakamakon rashin gudanar da zairga-zairgar da za su yi.
Ya jaddada cewa yan sanda za su kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
A karshe ya ce duk wanda ke da wani korafi ko kiran gaggawa na tilas, to sai ya kira 09052397880, 08024130926, 09051488448 da 07014951751, 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940839.
Discussion about this post