PDP ta yi barazanar kin amincewa da sakamakon zaben gwamnan Kaduna

0

Jam’iyyar PDP ta yi barazanar cewa akwai yiwuwar ta ki amincewa da sakamakon da ake kan tattarawa na gwamna da majalisar dokoki na jihar Kaduna, ba muddin bai yi daidai da abin da jama’a suka zaba ba.

PDP ta ta ce ba za ta karbi sakamakon zaben da aka tabka magudi ba.

Amma PDP ta ce har yanzu dai ba ta yanke shawara kan wace matsaya za ta dauka ba. Wato ko ta karbi sakamakon ko kuma ta yi watsi da shi.

Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Felix Hyet ne ya bayyana haka a wani taro da manema labarai da ya shirya yau Lahadi Kaduna.

Ya ce akwai rahotannin fizgen akwatinan kuri’u a wurare da dama kamar a Kananan Hukumomin Chukun, Giwa da Birnin Gwari.

“A wasu kananan hukumomin ma katin tantance katin zabe wato ‘card reader’ bai yi aiki ba, kuma akwai wurare da dama a Zaria inda aka rika sayen kuri’u a fili, a gaban jami’an tsaro.

Ya kara da cewa an tura dimbin jami’an tsaro a Kananan Hukumomin Sanga da Kagarko a Kudancin Kaduna don kawai a jirkita sakamakon zabe yadda zai faranta ran jam’iyya mai mulki.

Ya roki magoya bayan PDP da kada su tayar da hankula, su jira a fadi sakamako. Kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da na INEC su yi adalci.

Share.

game da Author