PDP ta roki kotu iznin bincikar kuri’un da kayan zaben shugaban kasa

0

Jam’iyyar PDP ta nemi Kotun Musamman Mai Sauraren Kararrakin Zabe ta ba ta iznin bincikar dukkan kayyakin da INEC ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa da ta tarayya.

Jam’iyyar ce da kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin ta, Atiku Abubakar ne suka gabatar da wannan bukata a jiya Talata.

Majiya daga Kotun Daukaka Kara, inda Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ke zama, ta tsegunta wa PREMIUM TIMES wannan bukata da Atiku da kuma PDP suka shigar.

Majiyar dai ba ta so a ambaci sunan ta, ta tabbatar da cewa ana sa ran za a zauna sauraren korafin da Atiku da PDP suka yi kafin karshen wannan mako.

“Wannan bukata ce suka nema ta kai-tsaye daga kotu, ba shigar da kara ce aka yi ba tukunna. Abin da suke bukata shi ne, a ba su damar bincikar kayan zabe, wanda a ciki ne za su kara tsamo wasu bayanan da za su hada su shigar da karar gadan-gadan.” Inji majiyar PREMIUM TIMES.

Wannan bukata da PDP da kuma Atiku suka shigar ta hannun lauyan PDP, Chris Uche, ta na nufin kotu ta ba su damar binciken kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zabe, wadanda suka hada da: Rajistar Masu Jefa Kuri’a, Na’urorin Tantance Masu Jefa Kuri’a, wato Smart Card Reader, kuri’un da aka jefa da sauran takardun bayanan da aka yi amfani da su wajen tattara sakamakon zabe.

An kasa samun Kakakin INEC na Kasa, Oluwole Osaze-Uzi domin a ji ta bakin sa.

Sai dai kuma da aka tuntubi APC domin jin ta bakin ta, ta bayyana cewa wannan bukata ce aka mika ga kotu, ba ga APC ba. Don haka baburuwan APC a wannan batun a yanzu tukunna.

Jam’iyya mai mulki, wadda kuma ita ce ta sake lashe zabe, ta ce ba ta damu ba, duk abin da PDP ke bukata daga INEC ta je kotu a ba ta izni ta duba.

Sai dai kuma APC ta ce kamata ya yi PDP ta bi tsari na doka kafin ta nemi iznin bincikar kayan zabe.

A cewar APC, ba a saurin gaggawar neman wannan izni sai fa idan magana ta rigaya ta je kotu, har an kai ga fara tankiya kan wani abu ko batu da ake da bukatar a bincika filla-filla domin a tantance tsaki da kuma tsakuwa.

Idan ba a manta ba, jam’iyyar PDP da shi kan sa Atiku duk sun ki amincewa da sakamakon zaben 2019, kuma suka ce ba wanda zai hana su garzaya kotu.

Share.

game da Author