Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, ta ki amincewa da zaben da ake ci gaba da gudanarwa yau a jihar Kano.
Ana gudanar da zaben ne a wasu rumfunan zabe a Kananan Hukumomi 28 daga cikin 44 na fadin jihar.
Shugaban Jam’iyyar PDP, Rabi’u Bichi ne ya bayyana haka da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Kano.
Ya ce PDP ba ta amince da zaben ba, saboda ya zo da hargitsi tare da kai wa magoya bayan PDP hari, hana su yin zabe da kuma ji wa da daman su raunuka.
Bichi yace dama tun a ranar Juma’a sai da ya ja hankalin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, inda ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki a Kano, wato APC, ta na jigilar mahara daga wasu jihohi zuwa cikin Kano.
Ya ce abin da ya faru yau Asabar a Kano, ba zabe ba ne, hauka ne, zubar da jini da kuma tauye wa dimokradiyya ‘yancin ta.
Ya ce daya daga cikin dan majalisar jiha wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Gwale, mai suna Babangida Yusuf an kai masa hari, kuma an jima mummunan rauni.
“Mun kuma samu rahoton kai wa magoya bayan mu hari a Kananan Hukumomin Doguwa, Gwale da Dala.”
Ya ce PDP za ta nemi hakkin ta a kotu.
Discussion about this post