PDP: An yi mana murdiya a Kaduna, zan garzaya kotu – Inji Isa Ashiru

0

Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna na Jam’iyyar PDP Isah Ashiru ya bayyana rashin amincewar sa da sakamakon Zaben gwamna da aka bayyana na Jihar Kaduna Inda gwamna Nasir El-Rufai yayi nasara.

Isah ya koka cewa an tafka magudi da aringizon kuri’u a wurare da dama musamman a kananan hukumomin Lere, Giwa, Birnin Gwari, Kubau, Ikara, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu da wasu da aka yi amfani da jami’an tsaro wajen taimakawa Jam’iyya mai mulki ta yi abinda ta ga dama.

” A wurare da dama an yi amfani da karfin mulki wajen muzguna wa masu Zabe don a kada mu a Zaben.

” Idan ka duba yadda aka bayyana sakamakon, wai a Zaben gwamna ne mutanen suka fito Zabe fiye da na Shugaban Kasa domin babu yadda za a ce wai gwamna ya fi samun yawan kuri’u a Kaduna fiye da Buhari. Kai ma kasan wannan hira ce kawai ba gaskiya ba.

” A Dalilin haka tuni har na mika korafina ga hukumar Zabe sannan kuma na shigar da karar rashin amincewa ta da sakamakon Zaben da Kuma kalubalantar sakamakon a kotun sauraren kararrakin Zabe .

Idan ba a manta ba tun kafin a bayyana sakamakon Zaben ne Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa akwai yiwuwar ba zata amince da sakamkon zaben ba.

Shugaban jam’iyyar Hassan Hyet tun a lokacin da ake zabe ya ce PDP ta gano cewa ana shirya yin magudi domin kayar da PDP a zaben gwamna na jihar.

Share.

game da Author