Ofishin Kamfen Din Buhari ya zargi PDP da shiga rumbun na’urar tattara sakamakon zaben INEC

0

Ofishin Kamfen Din Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi PDP da shiga rumbun na’urar tattara sakamakon zabe ta INEC.

Ofishin Kamfen din ya rubuta wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda da kuma Darakta Janar na SSS wasikar korafi da zargin samun damar shiga rumbun Na’urar da INEC ke adana bayanai sakamakon zaben Shugaban Kasa na 2019.

Kakakin Kamfen din, Festus Kiyamo ne ya rubuta takardar korafin, tare da cewa PDP ta karya dokar kasa.

Ya ce bayanai sun nuna cewa dama tun kafin zaben shugaban kasa na ranar farko kafin a dage zaben, PDP ta yi shirin dumbuza kididdigar sakamakon zabe na karya a cikin rumbun ajiyar INEC.

Atiku bayan yay i watsi da sakamakon zaben, ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben da ratar kuri’u milyan 1.6 wadanda ya ce ya bai wa Buhari.

A kan wannan dalilin ne Kiyamo ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda da kuma Darakta Janar na SSS takardar korafin cewa PDP ta wuce gona da iri.

Daga nan sai Kiyamo ya roki ofisoshin hukumomin tsaron biyu da su gaggauta bincken yadda PDP ta samu dabarar kutsawa cikin rumbun ajiyar INEC, duk dacdai ikirarin tsere wa APC da Atiku ya yi, ya tabbata karya ce, ba gaskiya ba.

Share.

game da Author