NAZARI: HARAJIN ‘VAT’: Kudaden Raya Kasa Ko Jiki-magayi?

0

Akasarin abin da talakawan kasar nan su ka dauka dangane da Shugaba Muhammadu Buhari kafin ya ci zabe a 2015, shi ne za a samu saukin rayuwa, fiye da wadda ake ciki a wancan lokacin.

Sai dai kuma jim kadan bayan hawan sa, sai labari ya fara shan bamban, domin ya kusa nunka kudin litar man fetur, dalar Amurka ta yi tashin gwauron zabo, haka kuma kayan abinci musamman shinkafa wasu na masarufi duk sun kara tsada.

Ba da jimawa ba kuma sai gwamnatin Buhari ta rika korafin cewa matsalar gwamnatin baya ce ta dabaibaye gwamnatin sa ta APC, shi ya sa aka kasa fita dagac cikin matsaloli.

Sai ya kasance duk inda Buhari ko Mataimakin sa Osinbajo su ka tsuguna, farkon abin da za su shaida wa jama’a shi ne gwamnatin APC ce ta jefa kasar nan cikin mawuyacin halin da ita gwamnatin Buhari din ta kasa fitar da jama’a.

Duk da karin kudin man fetur da aka yi, wannan bai sa gwamnatin ta yi hamdala daga tatsar kudade a jikin ‘yan Najeriya ba, sai da ta fara tunanin kirkiro kudaden haraji, da kuma hanyoyin tilasta karbar kudaden.

Tun a zamanin tsohuwar ministar harkokin kudade, Kemi Adeosun da aka kama da harkallar satifiket ne NYSC aka fara bijiro da hanyoyin kara tatsar kudade a jikin ‘yan Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta dora Babatunde Fowler a kan shugabancin Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS). Fowler ya jajirce wajen karbar haraji iri daban-daban a kasar nan.

Hakar gwamnatin Buhari wajen kokarin ta cimma ruwa wajen tara tulin kudaden haraji ya yi nasara, domin a ciki 2018, an bayyana cewa Hukumar FIRS ta tara naira tiriliyan 5.3.

A tarihin Najeriya dai ba a taba tara wadannan makudan kudade a matsayin harajin shekara dayaba. Amma cikin 2012 gwamnatin Goodluck Jonathan ta tara naira tiriliyan 5.07.

SAI MUN KARBI HARAJIN NAIRA TIRILIYAN 8 A 2019 –Shugaban FIRS

A farkon shekarar 2019 ne Shugaban Hukumar, Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, FIRS, Tunde Fowler, a wurin wani taro kan sha’anin kudaden haraji a Lagos, ya ce Najeriya ta kudiri aniyar tara har naira tiriliyan 8 a cikin shekarar 2019 da mu ke ciki.

Fowler ya ce an tara harajin naira tiriliyan 2.467 daga harajin da ba na harkoki danyen mai ba. sai kuma naira tiriliyan 2.95 daga kudaden shiga na harkokin mai a cikin 2018.

Abin mamaki, duk da wannan makudan kudaden da aka tara, shekarar 2018 ce gwamnatin Najeriya ta fi ciwo bashi a kasashen waje, musamman ta hanyar hadin-guiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin gudanar da wasu ayyukan da ke cikin kasafin kudi.

Har ila yau, a cikin 2018 din sai kuma gwamnatin tarayya ta sake lasar takobin kara tatsar haraji daga ‘yan Najeriya, tare da shan alwashin daukar ma’aikatan da za su rika bin kamfanoni, masana’antu da daidaikun mutanen da suka wajaba su biya haraji, domin su tilasta su biya.

‘VAT: HARAJIN JIKI-MAGAYI

Kwatsan a cikin watan Fabrairu, sai Shugaban Hukumar FIRS, Fowler da kuma Ministan Harkokin Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Udo Udoma, suka ce “Idan ana so gwamnatin tarayya ta rika samun kudaden da za a rika biyan karin albashin ma’aikata daga naira 18,000 zuwa naira 30,000, to fa tilas sai an kara kudin harijin ‘Valued Added Tax’, wato ‘VAT’.

‘VAT’ shi ne harajin kashi 5 bisa kashi 100 na duk wata mu’amalar kudade da dan Najeriya ko ma dan wata kasa keyi a cikin Najeriya.

Idan ma’aikacin gwamnatin tarayya, jiha ko karamar hukuma ne kai, to ana cire wa gwamnatin tarayya kashi 5 bisa 100 na albashi ka ba ta.

Idan ma ka na aiki a karkashin wani kamfani ne, to ana cire maka kashi 5 bisa 100 na albashi a bai wa gwamnatin tarayya.

Idan wata huldar kudade za ka yi a banki, to sai an cire wa gwamnatin tarayya kashi 5 bisa 100 na kudaden ka.

Idan ka shiga kantin sayen kayayyaki, ka yi ciniki, to akwai ‘VAT’ na kashi 5 bisa 100 da za a kara maka a kan kudin da ya kamata ka biya na kayan da ka saya.

Kai ko da a gidan cin abincin zamani ka shiga za ka ci shinkafa da wake ko alale, sai an dora maka kashi 5 cikin 100 daga kudin da ya kamata ka biya, a matsayin harajin ‘VAT’ ga gwamnatin tarayya.

A kan wayi gari a rana daya wani dan Najeriya zai biya haraji sau 10 ko sau 15 ga gwamnatin tarayya.

Duk wadannan fa ba su a cikin lissafin kudaden haraji na shekara-shekara da mutane ke biya. Kamar kudaden da ka ke biya ka sayi rajistar lambar mota, babur, takardun mota ko wadanda ake biya a mallaki lasisin tuki. Ko kuma wanda z aka biya domin a amince ka rika yin haya da motar ka.

Idan dan Najeriya ya kasance direba ne, to biyan dukkan wadannan haraji-haraji da aka lissafa a sama duk sun wajaba a kan sa. Sannan kuma sai ya biya harajin shiga tashar mota, harajin kungiyar ‘yan ‘union’ na mota. Kana kuma idan lodin dabbobi ya yi daga Maiduguri ko Kano ko Sokoto zuwa Lagos, duk jihar da ya keta sai ya biya haraji.

To duk wannan bai isa ba, sai da Udoma, Ministar Kudade Zainab Ahmed da Fowler suka kara kirkiro wa ‘yan Najeriya wasu hanyoyin da za a rika tatsar kudade a jikin su.

Na farko dai Tunde Fowler cikin mako biyu da suka gabata, ya ce za a kara yawan harajin ‘VAT’ karba daga kashi 5 bisa 100, zuwa kashi 7.5 bisa 100.

Sannan kuma ranar Alhamis, sai Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kammala shirin kirkiro hanyoyin kara karbar haraji ga ‘yan Najeriya, domin a samu kudaden da za a yi ayyukan raya kasa da ke cikin kasafin kudi na 2019.

PREMIUM TIMES ta ruwaito a ranar Laraba cewa, Gwamnatin Tarayya ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata, domin bijiro wa ‘yan Najeriya da sabbin hanyoyin karbar haraji.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, inda ta ce za a bijiro da hanyoyin ne domin samar wa gwamnati kudaden shiga.

Zainab ta yi wannan jawabi ne a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya na Kasafin Kudade.

Cewa ta yi ta haka ne za a kara samun kudaden shigar tafiyar da ayyukan Kasafin 2019.

Ministar ta ce an karkasa hanyoyin samun kudaden harajin zuwa gida uku, wadanda ta roki Majalisar Tarayya da su daure su bada goyon bayan shigo da sabbin hanyoyin da za a karbi harajin ga ‘yan Najeriya.

Ta ce hanya ta farko ita ce jajircewa da kuma tabbatar da an ci gaba da karbar haraji a inda duk ake ci gaba da karba a yanzu.

A wannan mataki ne Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakin toshe duk wata kofar da harajin da ya kamata a karba ba ya shiga aljihun gwamnati.

Sannan kuma akwai matakin hada kai da guiwa da masu zuba jari domin samar da kudaden da za a yi ayyukan makamashi da su.

“Hanya ta biyu kuma ita bijiro da sabbin hanyoyin da za a karbi kudaden haraji tare da tilasta wa wanda duk bai biya ya tabbatar cewa ya biya.

“Ina shaida wa Kwamitin Majalisar Tarayya cewa mun tsara hanyoyin bijiro da samun kudaden shiga ga gwamnati, ta hanyar kara hanyoyin karbar kudaden haraji, wadanda nan gaba kadan za mu dawo majalisa domin mu zauna tare da ku mu tattauna su. Haka kuma za mu kara harajin ‘VAT’’.

ZAINAB, UDOMA DA FOWLER SUN FUSATA ’YAN NAJERIYA

Wannan furuci na Zainab da na Fowler da Udoma, wadanda suka ce za a kara VAT domina samu kudaden da za a rika biyan karin albashi, ya harzuka ‘yan Najeriya da dama.

Da yawa su na cewa me ya sa gwamnatin APC ba ta tayar da wannan magana ba, sai bayan da aka bayyana an yi nasarar cin zabe? Me ya hana ta yi wannan karin kafin a yi zabe? Shin wannan ba yaudara ba ce? Ina alkawarin da Buhari ya yi cewa ‘yan Najeriya za su samu sassaucin rayuwa a zamanin mulkin sa?

Duk tambayoyin da ‘yan Najeriya ke ta yi kenan tun daga jiya har yau, watakila ma har zuwa nan da watanni masu yawa.

Cikin wadanda suka soki lamirin karin kudin haraji kan ‘yan Najeriya, har da jagoran APC, Bola Tinubu, wanda a jiya Alhamis wurin Taron Taya shi Murnar Cika Shekeru 67, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da kada a kara wa ‘yan Najeriya kudaden haraji.

Da ya ke magana a Dakin Taro na International Conference Center, Abuja, Tinubu cewa ya yi idan aka kara harajin, to karfin da takala ke da shi na sayen wasu kayan masarufi ko na abinci zai ragu sosai, zai kasa sayen wasu abubuwan, ko kuma ya saya, amma ba za su iya wadatar sa shi da iyalin sa ba.

Tinubu ya ce ko makawa babu, karin haraji tamkar karin wahala ce a kan ‘yan Najeriya.

Ita ma Kungiyar Kwadago ta Kasa, ta ce ba ta yarda don za a kara wa ma’aikata albashi ba, a ce sai an yi wa jama’a karin haraji.

Idan ba a manta ba, a lokacin da Shugaba Buhari ya sa hannun amincewa da karin mafi kankantar albashi daga naira 18,000 zuwa naira 30,000, ya ce jami’an da hakkin ke kan su su duba sosai su bijiro da hanyar da za a rika samun kudaden da za a rika biyan karin albashin.

YUNKURIN DORA WA IYAYEN DALIBAI HARAJI BAI YI NASARA BA

Idan za a iya tunawa, PREMIUM TIMES a cikin 2018 ma an yi yunkuri domin dora wa iyayen daliban yara ‘yan sakandare biyan haraji a duk shekara. Sai dai a bisa dukkan alamu, yunkurin bai yi nasara ba.

Domin a Taron Majalisar Kolin Harkokin Ilmi ta Kasa, karo na 63, a Abuja. A wurin taron dai an fito da wani shiri da Gwamnatin Tarayya ta fara tunanin dora wa iyayen daliban sakandire da firamare harajin kudin makaranta na tilas.

Idan da an amince da wannan tsari, iyayen yara za su rika biyan kudin makaranta a kan tsarin yawan ‘ya’yan ka, yawan harajin da za ka rika biya na kudin makaranta.

Gwamnati ta shigo da wannan tunani ne inda aka tattauna batun a Taron Majalisar Majalisar Kolin Harkokin Ilmi ta Kasa, karo na 63. Da farko har an rigaya an rattaba amincewa da shigon da tsarin biyan harajin, amma da gardama ta tirnike, tilas aka cire batun aka jingine shi gefe.

Idan da an amince da wannan tsari, to za a rika biya wa ‘yan firamare nira 500 kowane yaro, yayin da su kuma daliban sakandare za a rika biya wa yaro naira 1000.

Bayanin da ke kunshe da batun harajin wanda da farko aka rattaba amincewa da shi, ya nuna cewa za a rika biyan kudaden a cikin wani asusu da tuni har sun yi gaggawar rada masa suna ‘‘Asusun Tara Harajin Dalibai”.

Sai dai kuma ana tsakiyar taron sai wani babban jami’in harkokin ilmi wanda da ya mike bai ambaci sunan sa ba, ya ce idan har aka fito da tsarin biyan harajin ‘yan makarantar firamare da sakandare, to fa an karya dokar da ta kafa tsarin bayar da ilmi kyauta na bai-daya, wato Dokar UBEC ta 2004.

Shi kuma Karamin Ministan Ilmi, Anthony Anwukah, cewa ya yi batun kudin harajin dalibai abu ne da ya ke bukatar ya bi matakai ana tattauna shi, domin Hukumar na tattauna hanyoyin samar da harkokin ilmi kudade.

“Duk da cewa Dokar UBEC ta 2004 ta ce a bayar da ilmi kyauta, amma ai wannan doka za a iya yi mata ‘yar kwaskwarima ta yadda za a iya magance matsalar kudaden gudanar da harkokin ilmi a kasar nan.” Wannan jawabi na ministan na nuna cewa gwamnati na goyon bayan fito da tsarin biyan harajin daliban kenan.

Shi ma Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilmi, Sunny Echono, cewa ya yi dalibai da iyaye ne ya kamata su dauki nauyin taimaka wa harkokin ilmi a kasar nan. Sai dai kuma saboda an kasa cimma matsaya daya, tilas aka cire wannan batu, aka jingine shi.

INA ALKAWARIN BAYAR DA ILMI KYAUTA?

Wannan yunkuri na neman yanka wa iyayen yara harajin karatun ‘ya’yan su a makarantun firamare da sakandare da aka tattauna a ranar Alhamis, ya bai wa dandazon ’yan jaridar da ke wurin mamaki, domin kowa ya tabbatar da irin alkawarin da gwamnatin APC ta yi a lokacin kamfen cewa da zaran ta hau mulki, to ilmin kyauta ne, tun daga firamare har zujwa jami’a.

Baya ga wannan alkawarin, akwai alkawarin ciyar da ‘yan firamare, wanda ya zuwa kaarshen 2018 gwamnatin tarayya ta ce an ciyar da dalibai sama da milyan 8.5. Wannan shiri ya na fuskantar kalubale, ga shi kuma har yau a wasu wuraren ba a ma san ana yi ba.

Akwai kuma wani babban alkawari da APC ta yi cewa ta na hawan mulki ba tare da bata lokaci ba, za ta bi ilahirin makarantun sakandire na yankin jihohin Arewa-maso-Gabas ta zagaye su da Katanga, sannan kuma ta bi gaba dayan su a makala musu kyamara mai-gani-har-hanji, domin magance matsalar tsaro.

Wannan alkawari kuwa ya na neman zama tatsuniya, domin har yau ba a kara tada labarin sa ba, wasu kuma sun ma manta da cewa an yi shi.

A zaman yanzu tun daga biro da fensari da kayan litattafan karatu, duk iyayen yaro ke saye. Inda Allah ke kawo sauki musamman mu a nan Arewa, shi ne da ake samun wasu masu hannu da shuni ko kungiyoyin tsoffin dalibai da ke taimaka wa wasu makarantu da kayan aiki.

HARAJI: IDAN BA TA DORA TALAKA AKAN DOKI BA……

Idan mu ka koma batun haraji, mutane da daman na ganin cewa sai gwamnati da jami’an ta da masu rike da mukaman siyasa sun rage almubazzaranci kuma an rage musu albashi, sannan za a iya samun kudaden da za a rika cike gurabun cikas din kudaden yin ayyuka.

Kai, ko ba komai dai ya kamata gwamnatin APC ta fahimci cewa idan har ba ta dora talakan Najeriya a kan doki ba, to ba fa zai yiwu a lafta wa talaka kaya bisa kan sa ba!

Share.

game da Author