Karamin Ministan Harkokin Waje, Hadi Sirika, ya bayyana haramta wa jirgin nan samfurin Boeing 737 Max 8 yin sufuri a sararin saman ta.
Sirika ya yi wannan bayani ne sakamakon hatsarin da jirgi samfurin Boeing din ya yi cikin makon da ya gabata.
Jirgin wanda yay i hatsarin na kamfanin Ethiopian Airline ne, kuma dukkan fasinjojin sa 157 da ma’aikatan jirgin su shida, duk sun mutu.
Dama kuma wani jirgin samfurin Boeing din na Ethiopian Airline ya kashe mutane 186 a cikin watan Disamba da ya wuce.
Hadarin baya-bayan nan ya afku ne a kan hanyar jirgin daga Addis Ababa, babban birnin Ethiopia zuwa Nairobi, babban girnin kasar Kenya.
Cikin wadanda suka rasu har da mashahurin Farfesa Pious Adesanmi, wanda a yanzu haka a jihar sa ta haihuwa da Abuja, babban birnin tarayya, ake ci gaba da zaman alhinin rasuwar sa.
Minista Sirika ya bayyana hana jirgin zirga-zirga a Najeriya ne a a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan kammala taro Majalisar Zartaswa da aka gudanar jiya Laraba, tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Kafin wannan sanarwar sai da Sirika a ranar Talata ya sanar cewa a Najeriya babu wani kamfanin zirga-girgar jirage da ke amfani da irin wanda ya yi hadarin.
Ya ce an dauki wannan mataki ne domin bin sahun sauran kasashen duniya da suka dauki irin wannan mataki domin su kare lafiya da rayuwar al’umma.
Cikin kasashen da suka dakatar da samfurin jiragen har da China da Rasha da sairan kasashe da dama.