Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa murnar cin zaben da jam’iyyar APC ke yi ta kusa komawa kuka.
Saraki, ya ce APC za ta bar murna ta koma kuka nan ba da dadewa ba, domin murde zabe ta yi, ba nasara ce ta samu ba.
Ya furta haka ne a lokacin da ya ke jawabi a taron Masu Ruwa da Tsarin PDP, jiya Labara a Abuja.
Ya yi nuni da cewa duk duniya ta ga shirmen da APC ta yi a ranar zaben shugaban kasa, abin da ya ce a daina kallon PDP ce ta yi rashin nasara ita kadai.
“Ai Najeriya ce gaba daya aka murde wa zabe, ba jam’iyyar PDP ba. saboda duk duniya an ga shirmen da aka yi wai shi zabe a ranar zaben shugaban kasa.”
Ya kara da cewa irin yadda aka yi amfani da sojoji a wurin zaben, ya kunyata Najeriya a idon duniya matuka.
“Ka ta ba ganin inda aka yi zabe, amma su kan su wadanda suka ce sun yi nasara din suna jin kunyar nasarar da suka samu? Sai a Najeriya ake irin wannan shirmen.
Tuni dai Atiku Abubakar da jm’iyyar PDP sun ki amincewa da sakamakon zaben, sun kuma garzaya kotu.
Atiku ya yi ikirarin cewa rumbun na’urar INEC mai tattara sakamakon zabe ya nuna PDP ce ta yi rinjaye a kan APC da kuri’u milyan 1.6.
Sannan kuma ya ce ya na da tulin hujjojin da suka tabbatar da zai kayar da Buhari a kotu.
Shi ma Saraki ya bayyana cewa ba da kuri’u aka kayar da shi ba, amma dai gwamnati ce ta yi amfani da karfin ta, ta kayar da shi zabe.
“Ba da dan takarar APC na yi takara a jihar Kwara ba. da gwamnatin tarayya na yi takara, kuma ta yi min taron dangi, ta kayar da ni, amma ba da yawan kuri’u ba.” Inji Saraki.