Mun mika wa Buhari korafe-korafen Atiku – Abdulsalami

0

Tsohon Shugaban Kasa, Abdulsalami Abubakar ya bayyana sakamakon taron da kungiyar su Wanzar Da Zaman Lafiya a Kasa, ta yi da Shugaba muhammadu Buhari.

Ya ce sun ziyarci Buhari kuma sun gabatar masa da korafe-korafen da dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar ya gindaya musu, Atiku ya yi

Kwamitin Abdulsalami ya gana da Atiku tun a ranar Alhamis, a gidan sa da ke Abuja.

Yayin da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, bayan fitowa daga taron sirri da Buhari, Abdulsalami ya ce ‘yan Najeriya da dama sun nuna takaicin su da kuma bakin cikin wasu abubuwa da suka faru a zaben shugabann kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

Ya ce irin wannan korafe-korafen da aka tayar ne ya kai su ga ganawa da Buhari domin su gabatar masa da damuwar Atiku Abubakar dangane da zaben.

“Na shafa fadar cewa abin da ke gaban mu shi ne ci gaban al’ummar Najeriya da kuma zama lafiya. Domin duk lokacin da rikici ya barke, ba zai shafi Abuja ko mazauna Ikoyi a Lagos ba. Talakawa dai kadai ya ke shafa.

“To dadin da na ji shi ne da PDP ta ce za ta je kotu ta nemi hakkin ta dangane da abin da ta ce ya faru a zaben 2019 da ya gudana cikin makon da ya shige. Hakan shi ne hanyar da ta dace.

“Atiku bai gindaya wasu sharudda ba, ya dai bayyana masa damuwar sa kuma it ace muka isar ga Buhari. Dalili kenan mu ka zo kuma mu ka mika wa Buhari domin mu san abin yi.

Share.

game da Author