Jam’iyyar PDP ta bayyana kwarin-guiwar da ta ke da shi cewa za ta lashe dukkan zabukan gwamna da za a sake maimaitawa a wasu mazabu da rumfuna ko kananan hukumomi a kasar nan, a ranar 23 Ga Maris, 2019.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya ce duk wani kokarin da za a yi domin a murde zaben ko karfa-karfa tare da magudi, to jama’a ba za su yarda ba.
Ya abin kunya ne a yanzu bayan kammala zabe APC ta fito ta na kukan yadda ta kasance musu, alhali kuwa kowa ya ga yadda ita jam’iyya mai mulki din ta yi amfani da karfin sojoji wajen gudanar da zabe.
Duk da haka sai Kola ya ce amma PDP ta na da yakinin cewa za ta yi nasara a dukkan zabukan da INEC ta ce ba su kammalu ba.
“A jihar Benuwai jama’a sun nuna ba su son APC. Kuma dama tun tuni jihar ta PDP ce. Kuma mu na sane da cewa PDP ce ke da rinjayen magoya baya a mazabu da rumfunan akwati.
Da ya koma kan jihar Ribas kuwa, Kola ya ce a can ma kamar ture-kaza-kwashe-kwai PDP za ta yi, domin kafin a dakatar da tattara kuri’u, PDP na kan gaba da kuri’u 81,000.
Ya ce tun daga 1999 har zuwa yau jihar Ribas a karkashin mulkin PDP ta ke.
Ya ce a jihar Kano kuma kowa ya san tarihin al’ummar jihar ba su yarda su zabi mai wuwure kudaden talakawan su, kuma ba a yi musu wata barazana ko bude ido.
“Jihar Bauchi kuwa tuni an ma rigaya an zabi PDP. Don haka ko INEC ba za ta iya damalmala sakamakon zaben ba.
“INEC ta tabbatar da cewa a jihar Bauchi APC ta yi walle-wallen kuri’u, kuma ta kwato adadin kuri’un da aka sace.
Ya kuma yi magana a kan sauran jihohin da suka rage, irin su Sokoto da sauran su.