Mu yi hakuri mu jira zagaye ta biyun da za ayi, InshaAllah za mu yi nasara – Inji Abba Yusuf

0

Dan takaran gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya roki magoya bayan sa da su yi hakuri a jira a kammala zaben jihar Kano da aka bayyana bai kammalu ba.

A cikin takarda da ya fitar wanda kakakin sa Sanusi Dawakin Tofa ya saka wa hannu, Abba ya bayyana cewa idan suka yi hakuri komai zai zo ya wuce.

” An san mu da hakuri. Mu ci gaba da yin haka in Allah ya yarda muna a sama ko bayan an kammala zaben. Sannan kuma magoya bayan mu su sani cewa PDP ce ke kan gaba a sakamakon da aka bayyana mune a kan gaba kuma inda ma za a sake zabukan duk wuraren da muke da rinjaye ne aka soke.

” Ina kira ga wuraren da aka samu wadannan matsaloli da za a sake zabe su fito kwansu da kwarkwata su zabi jam’iyyar PDP a zaben.

Share.

game da Author