Ministan Ilmi ya tabbatar da an yi lalata da dalibi a Makarantar Yara Kurame ta Abuja

0

Ministan Ilmi Adamu Adamu ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne da aka yi zargin cewa ana cin naman mutane, lalata da yara, shan jinin mutane da ayyukan kungiyar asiri a Makarantar Kurame da ke Kuje, Abuja.

Amma kuma ya yarda da gaskiyar rahoton da ’yan sanda suka bayar cewa bincike ya tabbatar da wani malamin makarantar yayi lalata da daya daga cikin daliban.

Adamu ya fadi haka a Abuja bayan da ya karbi rahoton Kwamitin Musamman Na Binciken Zargin Lalata da Kananan Yara a Makarantar Kurame.

Ministan ya ce wata mata ce mai suna Hannatu Ayuba ta rubuta takardar korafin cewa an yi lalata da dan ta a makarantar musamman ta kurame, wadda mallakar hukumar ilmi ta Abuja ce.

Ya ce daga nan ne Ma’aikatar Ilmi ta kafa kwamitin mutum 17, ciki kuwa har da jami’an tsaro domin su tabbatar da gaskiyar zargin da Hannatu ta yi.

Ya ce an kuma umarci kwamitin da ya binciki sauran zarge-zargen da aka yi, wadanda suka hada cin naman mutane, kungiyar asiri da kuma shan jinin mutane a makarantar.

Ya kara da cewa likitoci 12 sun yi bincike a cikin dalibai 170 dga cikin yawan dalibai 830 na makarantar, amma ba a samu wata illar an taba yin lalata da sub a.

Amma rahoton ’Yan sanda ya bayyana yadda wani mai suna Sani Filo ya amince da cewa ya taba yin lalata da Imran Kanun. Haka shi ma wani malami a makarantar.

Jami’an ‘yan sanda sun ce tuni aka fara gurfanar da Sani Filo tun bayan da ya furta cewa ya yi lalata da Imran.
A halin yanzu dai ya na a tsare a kurkukun Kuje.

Sai dai kuma Minista Adamu ya nuna damuwar sa dangane da yadda kwamiti ya nemi Hannatu da ta je gaban sa ta yi karin haske, amma shiru ta ki bayyana, duk kuwa da gayayatar ta bas au daya da kwamitin yay i ba.

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi Hannatu Ayuba, ta ce ba ta da bukatar zuwa gaban kwamiti ta kara yin wani bayani, domin jami’an ‘yan sanda duk gudanar da wani binciken da ake bukata.

Don haka inji ta, sake nanata maganar zai kara tayar mata da mikin zuci ne kawai.

Rokon da ta yi shi ne a samar da yanayin da masu nakasa kamar kurame ko bebaye za su iya samun damar koyo fa fahimtar darussan ilmi, kamar yadda sauran yara ke wannan dama.

A Human Right Radio ne aka gabatar da shiri na awa daya cur, inda aka bai wa Hannatu Ayuba da mahaifiyar ta damar yin magana game da lalatar da aka yi da yaron su a makarantar.

An yi hirar da ita ne cikin watan Fabrairu.

Share.

game da Author