Mata na bata da mutunci, kullum sai ta lakada min dukan tsiya – Magidanci a Kotu

0

Wani magidanci mai suna Oluwatosin Bakare ya nemi kotun dake Mapo a garin Ibadan ta raba aurensa da matarsa Enitan kan yawan lakada masa duka da take yi.

Bakare ya ce tun da ya auri matarsa Enitan a 2018 ba ya samun kwanciyar hankali a cikin gidansa.

” Enitan bata gani ni na da gashi a ka kwata-kwata. Yadda ta ga dama so take yi abinta.

Sannan bata jin kunyar kowa ballantana tsaron Allah da wadanda ke gaba da ita domin a duk lokacin da ta ga dama takan lakada mun duka, ta keta kayan dake jikina a gaban kowa babu abin da ya sha mata gaba.

Ya ce a dalilin haka yake rokon kotu da ta raba auren su ganin cewa babu ‘ya’ya a tsakanin su bayan zaman aure na shekara bakwai da suka yi

Ita kuwa Enitan ta roki kotu da kada ta raba aure domin wai acewar ta tana son mijinta matuka.

” Na sani cewa idan na rabu da Bakare ba zan samu miji mai hakuri kamar sa ba. Na fara labtar sa ne tun bayan shawarar kara aure da faston cocin mu ya bashi sannan da rashin bani kula bayan na yi barin ciki.

A karshe alkalin kotun Henry Agbaje ya dage shari’ar zuwa ranar hudu ga watan Afrilu domin ma’aurantan su sake tattaunawa a tsakanin su da bayyana shaidu.

Share.

game da Author