Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta bayyana sanarwar cewa ta tura jami’an tsaro domin su binciki matsaloli da rahotannin kai farmaki da masu garkuwa da mutane suka yi a wasu kauyuka cikin Karamar Hukumar Lapai.
Kakakin ’Yan Sanda Mohammed Abubakar, shi ya bayyana haka a lokacin da ya ke hira da mamema labarai a Minna, babban birnin Jihar Neja.
“Muna ta kkarin gano ainihin gaskiyar abin da ya faru a yankin Lapai. Amma dai yanzu hankula sun kwanta, domin mun tura jami’ai da za su binciki lamarin.”
An ruwaito yadda wasu ‘yan bijilanti na yankin wadanda ba su so a bayyana sunayen su, suka ce mahara sun mamaye wasu kauyuka na cikin Karamar Hukumar Lapai.
“Mun yi gangami a yanzu za mu fafata da mahara kusan su 40, kuma kowanen su dauke da muggan makamai, tunda gwamnati ba za ta iya taimakon mu ba.”
Wadanda aka yi hirar da su dai su biyar ne, amma ba su ce sun kai wa ’yan sanda rahoto ko ba su kai musu ba.
Amma dai sun shaida wa manema labarai cewa ’yan ta’adda sun addabi kauyukan Mute, Egba, Gupa da kuma Abugi, duk a cikin Karamar Hukumar Lapai.
Sun ce mako daya kenan cur mahara na cin karen su babu babbaka a yankin, amma jami’an tsaro ba su ma san an mamaye yankin ba.
Sun ce an yi garkuwa da mutane da yawa, kuma sun ce sai an biya diyyar dukkan wadanda suka kama sannan za su sake su.