A wasan kwallon kafa na Champions League da aka buga ranar Talata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta zura wa takwarar ta ta kasar Jamus, Schalke kwallaye 7 babu ko daya.
Idan ba a manta ba, a wasan farko tsakanin wadannan kungiyoyi a Jamus, Manchester City ta doke Schalke da ci 3-2.
A jimla, Manchester City ta doke Schalke da ci 10-2 kenan da hakan yasa ta tsallaka zuwa zagayen kwata final.