Man fetur sharri ne, ba alheri ba ne ga Najeriya –Ooni na Ife

0

Babban Basaraken Yarabawa, Ooni na Ife, ya bayyana cewa babbar rashin sa’ar da Najeriya ta yi, shi ne samuwar man fetur da iskar gas a kasar nan.

Ooni Ogunwusi ya shaida haka ranar Juma’a a lokacin da tawagar Shugabannin Kungiyar Masu Wuraren Yawon Bude Ido suka kai masa ziyara a fadar da da ke Ile-Ife.

Shugabar kungiyar ce Bilikisu Abdul ta jagoranci tawagar, tare da rakiyar wasu ‘yan jaridu.

Basaraken ya ce saboda an samu garabasar man fetur, sai aka yi watsi da sauran hanyoyin samun kudaden da za a gina kasa da su, aka maida hankali kan fetur da iskar gas kawai.

Ooni ya ce cikin hanyoyin da aka yi watsi da su a baya, har da tsarin yawon bude ido da ya ce nan ma hanya ce ta samun kudaden shiga masu yawa.

Ya yi kira da da a bai wa fannin yawon bude ido domin akwai albarkar samun kudaden shiga a ciki sosai.

“Harkar yawon bude ido abu ne da na ke da sha’awa kwarai da gaske. Ba na wasa da ita. Don haka ya kamata mu hada karfi da karfe mu ciyar da ita gaba.”

Ya yi alkawarin cewa zai halarci gagarimin bikin Kalankuwar da za a gudanar a Kalaba cikin Disamba da kuma Taron Kungiyar NATOP na Kasa da za a gudanar cikin watan Afrilu.

Share.

game da Author