MAJALISAR DATTAWA: Sanata Ndume ya shiga takarar Shugaban Majalisar Dattawa

0

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Barno ta Kudu, ya sanar da aniyar sa ta neman shugabancin Majalisar Dattawa, kujerar da Sanata Bokola Saraki zai sauka ya bari daga ranar 29 Ga Mayu, 2019.

Ndume yay i wannan sanarwa ce a cikin wata wasika da ya aika wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole.

Ya aika masa da wasikar ce a jiya Litinin, 25 Ga Maris. Sannan kuma an nuna wa manema labarai kwafen wasikar wadda aka aika wa Oshimhole din.

A cikin wasikar, Ndume ya nemi sanya albarka daga bangaren jam’iyyar APC a takarar ta sa, kuma ya na mai amanna da cewa shiyyar Arewa maso Gabas inda ya fito ne suka cancanci samar da Shugaban Majalisar Dattawa.

Ndume, wanda shi ne tsohon Shugaban Masu Rinjaye, ya ce ya fito takarar mukamin ne saboda kudiri da zuhurin da ya ke da shi wajen taimakawa a habbaka tattalin arzikin kasar nan.

Ndume kuma ya yi Shugaban Masara Rinjaye a Majalisar Tarayya Zango na 6.

Baya ga Ndume, shi ma Sanata Ahmed Lawan gada Jihar Yobe, ya na neman shugabancin na Majalisar Dattawa.

Dama kuma Lawan ya nema a 2015, amma bai samu ba, sai aka zabi Sanata Bukola Saraki.

Share.

game da Author