BI NAN DOMIN SAMUN SAKAMAKON ZABE KAI TSAYE
Bayan gudanar da zaben gwamna a ranar 9 Ga Maris, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana jihohi shida cewa zaben su bai kammalu ba.
Jihohin sun hada Adamawa, Bauchi, Benuwai, Kano, Filato da Sokoto.
Cikin sharuddan zaben INEC, idan kuri’un da aka soke sun fi yawan wadanda na farko ya yi wa na biyu rata, to sai an sake zabe a inda aka soke kuri’u.
Haka idan aka yi tashin hankali ko hargitsin da aka dagula zabe ko sakamakon zabe, to sai an sake zabe a inda rumfa ko mazabar da aka yi yamutsin.
A jihar Bauchi za a sake zabe ne a rumfunan zabe 36, cikin Kananan Hukumomi 15. Kuma mutane 22,759 ne za su sake zaben.
Mutane 121,299 ne za su sake zabe a kananan Hukumomi 22 na jihar Benuwai.
Gwamna Samuel Ortom na PDP ya tsere wa Emmanuel Jime na APC da kuri’u 81,554.
A Kano Abba Yusuf na PDP ya tsere wa Abdullahi Ganduje na PDP da kuri’u 26,655. Za a sake zabe a cikin kananan hukumomi 28, inda mutane 128,831 za su sake zabe.
Jihar Filato kuma Gwamna Lalong ne ke gaba da kuri’u 3,413. Za a sake zabe tsakanin mutane sama 75.
A jihar Sokoto kuma Gwamna Aminu Tambuwal na PDP ke rinjaye da ratar kuri’u sam da 3000. Za a sake zabe a kananan hukumomi 22, inda mutane 75,403 za su jefa kuri’a.
Ku biyo PREMIUM TIMES HAUSA kai tsaye domin jin yadda ta kaya a zabukan da ake fatan kammalawa yau Asabar.
KANO:
A karamar hukumar Rimin Gado jihar Kano a mazabun da za a yi zabe wato mazabun Attawa, Tammawa, Dika, Gulu, Rimin Gado da Jilli mmutane sun iske duk an riga an dangwala takardun zabe kafin ma su iso wajen.
Amma kuma dan majalisar Gwale, Garba Disu ya sanar da hukumar Zabe da ‘yan sanda na Rimin Gado.
” Duk takardun zaben an riga an dangwala su.”
Wakilan mu dake jihar Kano sun bayyana cewa sun yi ta yin karo da dandazon ‘yan daba dauke da muggan makamai a wuraren zabe a Kano.
Wasu rumfunar ma masu zabe sun ce har an riga an yi musu zaben domin ko da suka isa rumfunar zaben sai suka iske an dangwala katin zaben kaf.
KANO:
Wasu ‘yan jarida sun sha da kyar bayan wasu gaggan ‘yan daba dauke da makamai sun fatattake su a daidai suna kokarin yi wa masu zabe tambayoyi gama da zaben.
Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa ba a bar su sun shiga wurin kada kuri’ar ba. Ya ce suna isa wurin aka fatattake da muggan makamai sannan kuma wasu.
Wani dan jarida ya bayyana cewa a masallaci ya fake bayan an fatattake shi da zarbebiyar takobi.
” Wannan abu dai da kunya matuka domin ace wai zaben ma da ya kamata a yi cikin kwanciyan hankali wasu sai sun tada hankalin mutane.
ZABEN SOKOTO: ’Yan sanda sun ci zarafin wakilin PREMIUM TIMES a Sokoto akan aikin sa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta bada hakuri ga PREMIUM TIMES bayan da wasu jami’an ta suka ci zarafin wakilin jaridar, mai suna Taiwo-Hassan Adebayo a Sokoto.
PDP ta ce ba ta amince da zaben da ake maimaitawa a Kano ba
Bichi yace dama tun a ranar Juma’a sai da ya ja hankalin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, inda ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki a Kano, wato APC, ta na jigilar mahara daga wasu jihohi zuwa cikin Kano.
TARWATSA ZABE: ‘ Yan Sanda sun kama kwamishinan ayyukan musamman na jihar Kano
‘Yan sandan sun kama Yakasai ne a daidai ya na kokarin tarwatsa zabe a rumfunar zabe da ke karamar Hukumar Dala.
BENUWAI: An ragargaza kayan zabe a Jihar Benuwai
An tare motocin a kan hanyar Zaki Biam, a lokacin da suke dauke da kayan Mazabar Azendeshi.
BI NAN DOMIN SAMUN SAKAMAKON ZABE KAI TSAYE
A sakamakon zaben da aka bayyana daga jihar Sokoto, jam’iyyar APC ce ke kan gaba zuwa yanzu
PU 004, Waziristan B Ward, Sokoto ta Arewa
APC: 156
PDP: 135
PU 012, Sarkin, Adar, Atiku Ward Sokoto Ta Kudu
APC: 187
PDP: 133
Gwadabawa LGA
APC – 187, PDP – 163
Shuni
APC – 652, PDP – 626
SAKAMAKON ZABE KANO:
Gwarzo LGA – APC: 2,784 PDP: 34
Madobi – APC- 908, PDP- 164
Bichi – APC 1969, PDP 39
Bebeji – APC 205, PDP 0
Rogo – APC 1033, PDP 162
Sumaila – APC 968, PDP 154
Wudil – APC 954, PDP 23
Karaye: APC 1317, PDP 27
Rano – APC 2337, PDP 37
Warawa – APC 501, PDP 152
Danbatta
APC 608
PDP 24
Takai
APC 4221
PDP 149
Minjibir
APC 2214
PDP 226
Albasu LGA
APC 1804
PDP 66
SOKOTO:
Kware LGA
APC – 211
PDP – 186
Wamakko LGA
APC – 417
PDP – 221
BI NAN DOMIN SAMUN SAKAMAKON ZABE KAI TSAYE
BAUCHI:
1. Mazabar Kagadama, karamar hukumar Dass
PDP – 358
APC – 184
2. Darazo
Mazabu 4
PDP – 749
APC – 824
3. Shira
Mazabu uku
PDP – 86
APC – 152
4. Bogoro
PDP – 478
APC -101
5. Giade
Mazabu 4
APC – 639
PDP – 532
6. Ganjuwa
PDP – 353
APC – 432
7. Ningi
PDP – 791
APC -758
8. Gamawa
PDP – 96
APC – 154
9. Itas Gadau
PDP 619
APC 421
10. Kirfi
PDP – 473
APC – 206
11. Misau
PDP – 312
APC – 111
12. Alkaleri
PDP – 444
APC – 264
13. Toro
Mazabu uku
PDP – 828
APC – 536
14. Katagum
PDP – 203
APC – 262
15. Jamaare Local Government
PDP – 54
APC – 74