MAIMAITA ZABE: Gwamna Lalong ya gana da Buhari, ya ce shi ke tare da nasara

0

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a yau Litinin.

Sun gana ne inda suka tattauna batun zaben gwamna na Jihar Filato wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce na jihar bai Kammalu ba.

A ranar Asabar mai zuwa ce za a sake zabe a wasu yankuna, mazabu da runfuna a jihohi shida, ciki har da Filato.

Ganawar sirri da Buhari ta zo ne dan lokaci kadan bayan da Buhari ya gana da Gwamna Mohammed Abubakar.

Dukkan gwamnonin biyu dai duk ‘yan jam’iyya mai mulki, APC ce.

Jihohin da za a sake zabe a wasu mazabun su, sun hada da Bauchi, Filato, Adamawa, Benuwa, Kano da Sokoto.

Gwamna Lalong ya na gaba da ratar kuri’u tsakanin sa da dan takarar gwamna na PDP, Jerry Useni.

Amma kuma INEC ta ce zaben bai kammalu ba, saboda yawan adadin kuri’un da aka soke sun haura yawan kuri’un da ke rata tsakanin Lalong da Useni.

A jiya Lahadi dai ne da yamma Buhari ya bayyana cewa ba zai yi katsalandan a sarkakiyar zaben da ya dabaibaye jihohin har shida.

Sai dai kuma Lalong ya shaida wa manema labarai cewa ya kai wa Buhari ziyara ce dangane da kokarin da ake yi wajen inganta tsaro da kare lafiyar jama’a a Filato. Amma ba su tattauna batun zabe ba.

“An tambayi Lalong cewa ba ya ganin jama’a za su rika goranta musu ganin yadda suke ta tururuwar zuwa wurin Buhari, kada a rika cewa tsoron faduwa zabe suke yi, shi ya sa suke so Buhari ya tallata su ya ce kowa ya zabi sak?

Lalong ya ce ko kusa, ba haka ba ne, shi ya sa na sha cewa ni na ma fi so da aka soke, yadda ko da sau nawa za a maimaita, to sai ya kayar da PDP.

Share.

game da Author