Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana ce za ta fadada binciken kan kuri’un da aka soke daga Karamar Hukumar Tafawa Balewa.
Kakakin INEC Festus Okoye ne ya bayyana haka, a bisa dalilan rahotannin da Kwamishinan Zabe na Kasa da ke Bauchi ya mika wa INEC din.
“INEC ta gano cewa akwai batutuwa da dama da ke bukatar a kara fadada bincikar su. Don haka sai hukumar ta kafa Kwamitin Bincike a bisa jagorancin Kwamishinan INEC na Kasa domin a warware matsalar.” Haka INEC ta ce.
Jami’in tattara sakamakon zabe na Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Dominion Anosike ta ce ‘yan bangar siyasa sun kwace sahihin kwafen sakamakon zaben, wato Form EC 8C 1.
Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Mohammed Kyari ne ya ki amincewa da sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Bayan da aka yi zargin ‘yan bangar siyasa sun hargitsa dakin taron da ake tattara sakamakon zaben.
Anosike ta ce akwai sakamakon zabe na wata mazaba guda daya da aka keta kwafin takardar da ya ke ciki, sai ta yi amfani da kwamfuta ta rubuta sakamakon.
Sai dai kuma shi Kyari, ya ce ba zai yi amfani da sakamakon wanda ta rubuta ba, domin kafin ta zartas da hukunci ba ta tuntube shi ba. kuma ya ce ba ta nemi izni ko shawarar Kwamishinan Zabe na Jihar Bauchi ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa INEC ta kafa kwamitin bincike a karkashin jagorancin Festus Okoye, kuma har kwamitin ya gana da masu ruwa da tsaki a zaben. Kuma za su mika sakamakon binciken da suka gano ga INEC.
PREMIUM TIMES ta gano cewa tunda dai an bi duk abin da ya dace wajen gudanar da zabe da kuma tattara sakamakon zabe. Abin da kawai ke matsala shi ne yadda Anosike ta yi amfani da alkaluman cikin kwamfuta, maimakon na kan kwafen takarda a wata mazaba.
A kan haka INEC ta ce a sake hada sakamakon Karamar Hukumar Tafawa Balewa a kamar yadda ya ke.
INEC ta ce ta yadda za a yi hakan kuwa shi ne yin amfani da kwafen dafkal, wato na duplicate din sakamakon zabe na kowane matakin tattara sakamakon zabe kama tun daga rumfar zabe, mazaba da akwatin zabe.
Irin haka ne INEC ta yi a makon da ya gabata a Karamar Hukumar Nasasarawa cikin Jihar Kano, bayan da aka kekketa takardar da ke dauke da sakamakon zabe.
ABIN DA ZAI BIYO BAYA
Matsawar aka yi haka kuwa, to babu yadda za a yi jam’iyyar APC a karkashin Gwamna Muhammed Abubakar ta yi nasarar cin zabe a jihar Bauchi.
Saboda an rigaya an tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 19 daga cikin 20. A hakan, akwai ratar kuri’u 4,059 tsakanin Bala Mohammed na PDP, wanda yayi wa Gwamna Abubakar rata da su.
APC na da kuri’u 465,453 ita kuma PDP na da 469,512.
Idan aka koma karamar hukumar Tafawa Balewa kuwa, sakamakon da aka rigaya aka bayyana sun nuna cewa PDP na da 40,010, ita kuma APC na da 29,863. A nan ma an tsere wa APC, sannan idan an hada, an tsere wa APC da kuri’u 14,207 kenan.
Daga yanayin yadda jama’a ba suka fitowa zabe, jama’ar da za su sake zabe a mazabar da za a sake, ba su wadatar wa APC samun sakamakon da za ta ita galaba a kan PDP ba.
An tambayi Sakataren INEC rotimi Oyekanmi dangane da wannan dambarwa ta Jihar Bauchi, sai ya ce abinciken PREMIUM TIMES ba gaskiya ba ne.