Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce katafaren Cocin Dunamis din nan na Kaduna ya kauce wa dokokin iznin bin ka’idojin gine-gine na jihar Kaduna.
Hukumar Tsara Gidaje da Gine-gine ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ce kwanan nan ta rubuta wasiku ga daidaikun jama’a, kamfanoni da masana’antu da kuma kungiyoyin addinai cewa su gabatar mata takardun shaidar mallakar gine-ginen su.
Cocin Dunamis na daya daga cikin wadanda Shugabar Riko ta KASUPDA, Fatima Bambale ta rubuta wa wasikar, mai lamba PD/14/PP/ZIII/20,624/VOL I/0.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa maimakon Cocin Dunamis ya gabatar da takardun da aka tambaya ya bayar, sai ya kai karar gwamnatin jihar Kaduna a gaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), Reshen Jihar Kaduna.
Sakataren CAN na Jihar Kaduna Sunday Ibrahim, kuma sai ya rubuta wa KASUPDA cewa ai kamata ya yi KASUPDA ta nemi bayani daga Dunamis ta hannun CAN, ba wai kai-tsaye ta rubuta wa Cocin Dunamis din wasika ba. Sunday Ibrahim ya ce wasikar bai kamata a rubuta ta ba.
Sunday Ibrahim ya rubuta wa KASUPDA amsa ce a ranar 7 Ga Fabrairu, 2019, kuma wata babbar jaridar kasar nan ta buga labarin da wasikar ta kunsa.
Wasikar ta ce Gwamnatin Jihar Kaduna na so ta yi amfani da Hukumar KASUPDA domin ta ci zarafin Cocin Dunamis Reshen Jihar Kaduna ne kawai.
Amma kuma, a cikin wasikar da PREMIUM TIMES ta ci karo da ita, KASUPDA ta shaida wa Hukumar Kula da Tsarin Raba Filaye (KADGIS) ta Jihar Kaduna cewa Cocin Dumamis da ke karkashin Mazabar Farin Gida, a unguwar Mando, cewa “gidan haya ne, kuma ba shi da takardun shaidar izni gini.”
Takardar ta kara da cewa shi ma Ginin Cocin Dunamis da ke Command Junction, sai kwanan nan a ranar 14 Ga Janairu, 2019 ya aika ta takardar neman iznin gini.
Takardar wadda Daraktan Riko na hukumar, mai suna Bello Ibrahim ya saw a hannu, ta ce shi ma Cocin Dunamis da ke Gonin Gora, an nemi a ginin haya ne aka karba aq hannun wani mai suna Eromosele Emmanuel.
Takardar ta ce tun a ranar 8 Ga Oktoba, 2012 Emmanuel ya nemi iznin a ba shi damar gina coci, amma aka ce sai ya kawo takardun hakkin mallaka tukunna. Shi ma shiru ka ke ji har yau.
Shi ma Cocin Dunamis na Mararaban Rido, ba shi da takardun iznin gini.
Kokarin da PREMUM TIMES ta yi domin jin ta bakin jami’an Cocin Dunamis ya ci tura.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ji ta bakin Shugaban CAN na Jihar Kaduna, Joseph Hayeb, domin jin dalilin da ya sa kungiyar CAN din ta shiga cikin batun da ya shafi gwamnatin jihar Kaduna da Cocin Dunamis na Kaduna.
Joseph Hayeb ya ce “batun duk siyasa ce kawai, ni kuma ba na son jefa kai na cikin batutuwa na siyasa a daidai wannan lokaci da mu ke ciki.”
Ita kuma Hukumar KASUPDA ta ce ba Cocin Dunamis kadai aka raba wa wadannan takardun neman bayanai ba, har da sauran coci-coci da masallatai.
Amma shi kuma Hayeb ya kamata ya yi a raba waskikun kai tsaye ga hedikwatar Dunamis, ba a aika wa cocin da ke Farin Dida shi kadai ba.
Ya kara da cewa kuma akwai kungiya da ake tuntuba domin maslahar da ta shafi tattauna batutuwan da su ka shafi wannan addini da wancan, wadda ya kamata ya yi a ce ita aka fara tuntuba.