Mahara sun saki jami’an zaben da su ka yi garkuwa da su a Katsina

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce an sako ma’aikatan wucin-gadi na INEC da mahara suka kama a jihar Katsina.

Idan ba a manta ba, mahara sun kashe dan sanda daya suka kama ma’aikatan zabe uku a karamar hukumar Danmusa.

Kakakin ‘Yan sandan Katsina, Gambo Isa ya ce wadanda suka kubuta din kafin a hada su da iyalan su a gidajen su, sai da aka kai dukkn su asibitin Danmusa, inda aka duba lafiyar su.

Ya ce jami’an tsaro na kokarin kamo wadanda ke da alhakin sace su.

Tuni aka bayyana sakamakon zaben zaben gwamna a jihar ta Katsina, inda Gwamna Aminu Masari na APC ya kayar da Sanata Lado na PDP.

Share.

game da Author