A ci gaba da wasan Zakarun Turai da aka kammala zagaye na biyu a daren jiya, wasu manyan kungiyoyi sun sha dukan tsiya a kokarin sun a neman kai wa zagaye na uku.
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila ta dankara wa Bayern Munich ta Jamus ci 3:1 a birnin Liverpool. A wasan da suka fara bugawa a birnin Munich makonni biyu da suka gabata, an tashi canjaras, ba a ci kowa ba.
Kokarin da ‘yan wasan Liverpool, Sadio Mane da Virgil van Dijik su ka yi, ya kai sun zura wa Munich kwallaye uku su biyu.
Mane ya ci biyu, Dijik ya ci daya, yayin da Bayern din ta yi sa’ar rage haushi, inda ta jefa kwallo daya kadai.
Mai sharhin wasan kawallon kafa, Steve Nicol, ya ce duk da wannan nasara da Liverpool ta samu, wasan da ta ke bugawa bai kai karfi da ingancin irin wanda ta rika bugawa a kakar wasan da ya gabata ba, wanda ya kai ta ga buga wasan karshe ita da Real Madrid.
Ya kara da cewa akwai jan aiki a gaban Liverpool muddin ta na so ta sake kai wasan karshe, har ta yi nasara.