A jiya Alhamis ne Hukumomin Tsaro na ‘yan Sanda da Sojoji suka yi sanarwar cewa sun kama mutane 1,119 da ke da alaka da aikata laifukan da suka shafi karya dokokin zaben 2019 a Najeriya.
Kakakin Rundunar ‘Yan sanda na Kasa, Frank Mba ne ya yi wannan sanarwar a Abuja a wani taron hadin-guiwa da aka gudanar tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Hedikawar Tsaro ta Kasa.
Mba ya ce dukkan su a kama su ne a wurare daban-daban a lokautan zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya, wanda aka gudanar a ranar 23 Ga Maris da kuma zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 Ga Maris.
Ya ce an kama masu laifuka 796 a lokacin zaben gwamna da na majalisar dokoki. Sannan a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya kuma an kama mutane 323.
An kama 256 a Akwa Ibom, 117 a jihar Imo sai kuma 109 a jihar Kaduna.
Ya ce ana ci gaba da bincike, wanda binciken ne zai iya rage yawan wadanda ake zargin ko kuma ya kara yawan na su.
Mba ya yi jawabi ne a madadin sauran kakakin yada labarai na Hukumar Tsaro, Onyema Nwachukwu, na Sojojin Ruwa da na Sojojin Sama.