An rika watsa bidiyo da hotunan Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa, Godiya Akwashiki, a soshiyal midiya wadanda aka yi masa zigidir, bayan zargin kama shi da kokarin neman wata mata.
An kama Godiya Akwashiki ne ya na kokarin kwanciya da matar tsohon sakataren Hukumar Kula da Shari’a ta Kasa, Danladi Halilu, da aka sani da ‘Envuluanza.’
Cikin makon jiya ne aka zabe Akwashiki sanatan Nasarawa ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.
A cikin bidoyon, an ga yadda zababben sanatan ke ta rokon a ba shi ruwa ya sha. Can daga sama kuma ana jin wata murya wadda aka tabbatar da cewa ta Danladi din ce.
Wata majiyar da ke da kusanci da iyalan Envulanza ta tabbatar wa PREMUM TIMES cewa Akwashiki ya amsa laifin sa a gaban ‘yan sanda na kokarin neman ya kwanta da matar Danladi.
Akwashiki ya ce laifin shaidan ne, amma ba halin sa ba ne. Haka ya bayyana a ofishin ‘yan sanda na Maitama, Abuja.
Majiyar ta ce Akwashiki ya samu lambar matar ya rika buga mata waya da nufin ta roki mijin na ta ya goya masa baya domin ya samu nasarar zama sanata.
“Bayan ya ci zabe kuma sai ya rika damun ta da waya, kamar sau uku ko ma sau hudu a rana daya. Ganin inda ya karkata, wato neman yin lalata da ita ya ke yi, sai matar ta gargade shi har sau biyu cewa ya kiyaye ta.’ Haka majiyar mu ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Majiyar ta ce saboda idon Akwashiki ya rufe ya na son sai ya kwanta da matar, sai ya ki daina damun ta da yawan kira.
Ya ce a ranar da abin ya faru, Akwashiki ya kira maigadin gidan Danladi a Abuja da kuma direban Danladin, domin ya ji shin Danladi ya na Abuja ne ko kuwa?
Duk su duka biyu din suka ce masa Danladi ya yi tafiya zuwa Jos.
Akwashiki bai san Danladi da matar sa sun shirya masa tarko ba, su ne suka ce a ce shi Danladi din ba ya gari.
“Nan da nan sai Godiya Akwashiki ya kira lambar matar Danladi, ya mata ga inda ya ke so su hadu, a Exclusive Stores Super Market, inda zai sayi kayan shaye-shaye masu sanyi kafin su wuce otal din da ya kama.
“Bayan sun yi mahada a super market din, ya dauke ta a mota ne, aka bi su a baya aka kama shi, aka yi masa dukan tsiya, kuma aka yi masa tsirara ko dan kamfai ba a bar shi da shi a jiki ba. Daga nan aka damka shi a hannun ‘yan sanda na ofishin Maitama, Abuja.
PREMIUM TMES HAUSA ta mallaki hotunan Akwashiki da bidoyon da ya ke tsirara , bayan ya sha jibga kamar kurar roko.
“A hannun ‘yan sanda, Godiya Akwashiki ya amsa aifin kokarin kwanciya da matar Danladi a cikin takardar maida bayanin da ya rubuta da hannun sa.”
PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na kasa sun je ofishin ’yan sandan a wurin zababben sanatan, kuma a gaban su ya rubuta takardar furucin cewa ya yi kokarin yin lalata da matar.
Majiya ta karyata cewa wai gadar zare ce aka shirya wa Akwashiki.
Majiyar ta ce shi ne da kan sa ya rika damun ta kuma akwai shaidar muryar sa da sakonnin tes da ya rika yi mata masu dauke da kalamai na neman yin lalata da ita, duk an samu a cikin wayar sa.
Sai dai kuma magoya bayan sa sun ce sharri aka yi masa, don a wulakanta shi, domin sai da aka tsare shi da bindiga kafin a yi masa tsirara.
PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin sa, amma duk lokacin da aka kira wayar sa, ba ya amsawa.
Kakakin ‘yan sandan Abuja, Anjuguri Mamza, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana nan ana ci gaba da bincke.
Discussion about this post