Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zama Gwamnan Jihar Kano cikin 1999, a karkashin jam’iyyar PDP, bayan kasancewar sa kafin sannan ya taba rike mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, a zangon siyasar da aka yi karkashin mulkin sojoji.
RIGIMAR KWANKWASO DA RIMI
Farkon hawan Kwankwaso kujerar mulki, ya fara da samun matsala da iyayen gidan siyasar PDP, su marigayi Abubakar Rimi, sakamakon wani tsaurin idon da Rimi ke ganin cewa Kwankwaso ya yi masa a matsayin sa na gwamna.
Abin da kuwa ya faru shi ne, kafin zaben 1999, PDP kan yi tarukan siyasar ta a Gidan Akida, wanda gida ne na taron siyasar Rimi, amma daga baya ya rikide na PDPin jihar Kano bai-daya a lokacin.
An ci gaba da taruka a Gidan Akida har bayan hawan Kwankwaso gwamnati. Ba a dade ba sai Kwankwaso a matsayin sa na gwamna, ya ce tunda Gidan Akida gidan siyasa ne na bangaren mutum daya, wato Rimi, to bai kamata a rika taro a can ba. Musamman tunda PDP ta kasu bangare-bangare a Kano.
Kwankwaso ya ce a rika yin taro a ofishin jam’iyya maimakon a Gidan Akida. Wannan dauke taro da ya yi zuwa ofishin jam’iyya ya bata wa Rimi rai matuka.
Sabani ya shiga tsakanin Kwankwaso da Rimi, har ta kai ‘yan siyasa sun rika zuzuta rikicin, yadda ya kara tsami sosai.
Cikin fushi, kuma a cikin 1999, Rimi ya rubuta wa Kwankwaso wata wasika mai dauke da bayanan cewa: “Rudanin da ka ke haifarwa a cikin jam’iyyar PDP a Kano, da kuma masaniyar da na ke da ita cewa takardar shaidar digirin ka na Dakta ta bogi ce, to za su iya janyowa a tsige ka.”
KARSHEN ZANGON SA NA FARKO, 2003
Kwankwaso ya kammala zangon san a daya a cikin yanayin da guguwar Buhariyya ta fara bugawa a Kano. Hakan ya kawo karshen mulkin sa, inda APP ta tsaida Ibrahim Shekarau, tsohon ma’aikacin Kwankwaso, kuma ya yi nasara a kan sa.
An nuna wa Kwankwaso kiyayya a lokacin zaben a Kano. Ranar da aka sanar da sakamakon kayar da shi a zaben 2003, an yi ta kade-kade da karakainar murna a Kano har kusan wayewar gari.
Allah ya rufa masa asiri, inda shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ya nada shi wani mukami, daga baya kuma aka ba shi Ministan Tsaro. Duk a wadannan lokutan ya ci gaba da tafiya tare da Abdullahi Ganduje, wanda shi ne mataimakin sa a lokacin da ya ke gwamna.
KWANKWASO DAWO DAWO
Bayan Shekarau ya kammala zangon sa na biyu, cikin 2011, Kwankwaso ya koma neman sake hawa kujerar gwamnan Kano, kuma Kanawa suka yi masa kyakkyawar tarba. Ya sake karbar mulki a hannun Shekarau, wanda ya mika wa mulki a cikin 2011.
KWANKWASIYYA AMANA
Sake hawan Kwankwaso ke da wuya sai ya karfafa gidan akidar siyasar sa ta Kwankwasiyya. Da ya ke PDP ta kasu gida-gida ko a Kano, to shi Kwankwaso in dai ka na tare da shi, to ka bi Kwankwasiyya kawai. Haka ya gidan bangaren sa har cikin 2014, lokacin da wasu gwamnoni suka yi wa PDP tawaye, suka shiga APC domin mara wa Buhari baya. Cikin su kuwa har da Kwankwaso.
KAFA GANDUJE A KANO
Bayan kammala zangon Kwankwaso na biyu, ya tsaida mataimakin sa Abdullahi Ganduje takara a karkashin APC, kuma ya yi nasara. Shi kuma Kwankwaso ya ci kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Bayan Ganduje ya zama gwamna, yay i wa Kwankwaso godiya a gaban jama’a, inda ya ce ubangidan sa Kwankwaso ya rufa masa asari, a yau wai shi Ganduje, bagidaje, bakauye, Bafulatanin daji mai kiwo, mai yawo da karnuka, amma a yau shi ne gwamna a Kano.
Sai dai kuma tun tafiya ba ta yi nisa ba, aka samu mummunan sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje. Sabanin ya zama gabar da ta kai Kwankwaso ya shafe shekaru uku bai shiga Kano ba, gudun fitina tsakanin mabiyan sa da mabiyan Ganduje.
Sake kada gangar siyasar 2019, wadda Kwankwaso ya sake neman takarar shugaban kasa a karkashin PDP, bayan ficewar sa daga APC ya koma PDP, bai yi nasara ba, saboda Atiku Abubakar ya kayar da shi da sauran ’yan takara duka.
Kwankwaso bai nemi sake tsayawa takarar sanata ba, sai ya nemi sake kafa kan sa a Kano, ta hanyar farfado da akidar Kwankwasiyya. Ya yi kokarin ganin cewa sai aminin sa ya zama dan takarar PDP a jihar Kano. Kuma hakan ta kasance.
Dukkan jiga-jigan PDP da sauran wadanda suka nemi takara ba su samu ba, sun koma bayan Gwamna Abdullahi Ganduje, kuma karkashin tutar Buhariyya.
Wannan ya sa an yi wa PDP mummunan kaye a Jihar Kano, a zaben shugaban kasa da na Majalisar Dattawa da na Majalisar Tarayya.
A gaskiya kowa ya dauka siyasar Kwankwaso ya kare kenan a Kano, ko kuma ma a ce ta mutu. Duk da irin goyon bayan da Kwankwaso ke da shi, ganin yadda ya sha kaye a zaben shugaban kasa, an dauka a zaben gwamna ma haka za a yi wa Kwankwasiya dukan tsiya wanda zai hana ta sake mikewa tsaye.
FARIN JININ ABBA DA BAKIN JININ GANDUJE
Jam’iyyar PDP a Kano ta yi farin jinin samun dan takarar gwamna, wato Abba Kabiru Yusuf, da ake wa lakabi da Abba Gida-gida, daga wani salon wakar sa kamfen din sa da aka yi masa.
A gefe daya kuma Ganduje ya yi bakin jini saboda zargin sa da cika aljifan sa da milyoyin daloli da bidiyonya nuna ya na yi. wannan ya sa PDP ta samu kur’u fiye da APC kuma fiye da wadanda ta samu a zaben shugaban kasa.
KAI KADAI GAYYA
Kwankwaso ya koma Kano cikin watanni kadan da suka gabata domin sake shirin yakin siyasa. A cikin wannan dan takaitaccen lokaci kuma ya tabbatar da cewa shi kwamanda ne cikakke wanda sai da shi ake iya cin yaki. Kakaf a Najeriya yanzu hankalin kowa ya koma a kan makomar zaben Jihar Kano. Wanda kuma kowa ya san Kwankwaso ne ya kai zaben kasancewa yadda ya kasance a yanzu.
Kamar yadda Yasir Ramadan Gwale, wani dan gaban-goshin takarar gwamna Salihu Takai ya fada a Kano, ya ce: “Yanzu dai Kwankwaso ya mayar da kowa makaranta domin koyar darasin siyasa a jihar Kano. Tun daga Mundubawa har zuwa State Road, tun daga Darul Tauheed har zuwa gidan Akida kowa zai koma ya dauki darasi.”
“Kwankwaso shi kadai ya kara da gwamnoni uku, wato Abdullahi Ganduje, Ibrahim Shekarau da kuma Kabiru Gaya. Sannan ya kara da mataimakan gwamnoni uku, wato Nasiru Gawuna, Hafizu Abubakar da Abdllahi T. Gwarzo. Sannan ya kara da sanatoci shida da suka hada da Barau Jibrin, Lado, Zarewe, Hayatu, el-Doguwa da kuma Bello.
“Wannan fa banda tarin kwamishinoni na da da na yanzu, da ‘yan majalisar tarayya na da, da na yanzu, da tarin ‘yan siyasa da suka kunshi ciyamomi na mulki da na jam’iyya da kansiloli zababbu da nadaddu. Da gungun ‘yan siyasar da suka tattaru a gindin Gwamna Ganduje baya-bayan nan, duk Kwankwaso shi kadai ya tattara su ya murkushe.” Inji Sharada.
Jiya Lahadi da dare INEC ta bayyana Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara. Idan aka dubi yadda zaben da aka maimaita ya zo da kwamachala da kuma irin yadda aka rika kiraye-kirayen a soke zaben. Za a iya cewa akwai sauran rigima a kotu.
Su kan su kungiyoyin kare dimokradiyya sun yi Allah-wadai da yadda aka rika amfani da muggan makamai wajen tarwatsa jama’a a wurin zabe. Dama kuma jam’iyyar PDP ta tsine wa sakamakon zaben da aka bayyana. Kenan, akwai sauran kallo a kotu.
Ko ba komai dai, bayyana Ganduje wanda ya yi nasara, zai sa shi samun damar yin barci mai nauyi, akalla kafin a sake sabon lalen kokawa a Kotun Sauraren Kararrakin Zabe.