KWANKWASIYYA: Guguwar da ta kasa kayar da daurin tsintsiya ko guda daya

0

Duk da cewa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso ba kanwar lasa b ace, musamman idan aka yi la’akari da yadda bayan kayar da shi a zaben gwamna a 2003, sai da ya sake komawa a kan kujerar sa ta gwamna cikin 2011, hakan bai sa Kwankwaso ya sake irin wannan tasiri a Kano a zaben shugaban kasa na 2019 ba.

Irin yadda guguwar Kwankwasiyya ta yi farin jini wata biyu kafin zaben shugaban kasa a Kano, kowa ya yi tsamani guguwar za ta bi ta kan duk wata tsintsiya mai girma ko karama, wadda aka daure tamau ko wadda aka daure sako-sako, duk ta fatattaka su.

Duk da tsoron da guguwar Kwankwasiyya ta rika bai wa APC kafin zabe, abin mamaki sai ga shi ta yi faduwar tsohuwar tasa, wato ta fadi ba nauyi.

Kuri’un da PDP ta samu a zaben shugaban kasa a Kano, ba su isa a kira su kuri’un da a bugi kirji a ce an yi abin a zo a gani ba.

Baya ga cewa PDP ba ta tashi da ko da sanata daya ko dan majalisar tarayya a Kano ba, hatta kujerar Sanatan da Kwankwaso ke a kai, wadda Hon. Ali Madaki ya yi takara, sai da aka kayar da shi.

Kujerar ce tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya lashe. Kenan shi ne zai maye gurbin Kwankwaso a Majalisar Dattawa daga 2019.

Babu wata gadarar da Kwankwasiyya za ta iya yi yanzu a Kano, matsawar ba ta jajirce ta ci kujerar gwamnan jihar Kano ba.

Sai dai ita ma kujerar gwamnan za a iya cewa ta na kasa ta na dabo, domin a yau Litinin ne Babbar Kotun Tarayya ta ce ta soke takarar gwamnan da PDP ta shiga a jihar Kano.

Abin da ya rage wa PDP a Kano shi ne jiran sakamakon karar da su ka daukaka a yau din. Sai dai kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a yau ita kuma ta ce Abba Yusuf na PDP shi ne ta sani a matsayin dan takarar PDP a Kano ba wani ba.

Abin ya zame wa PDP goma da ashirin a Kano, wato ga gudu, ga nauyin kayan da ta ke dauke a ka, sannan kuma ga zanin da ta rufe katarar ta ya na neman ballewa.

Share.

game da Author