Kwankwasiyya Da Gandujiyya, Kowa Ya Rungumi Carbi Ya Tafi Kotun Allah, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Alhamdulillah ala kulli halin, Allah Ubangiji ya kawomu lokacin da zamu sake inganta imaninmu. Zaben 2019 yazo da sabon abu, mun yi kokari matika a kungiyance da kafofin yada labarai iri iri wajen fadakar da mutane akan siyasa da hanyoyin kawo gyara musamman basu shawara akan fitowa su yi zabe. Masha Allah, mun samu hadin kan matasa gaskiya amma saidai za6en yazo da akasi wanda muke rokon Allah ya kawo karshen abun da ikonsa da iyawarsa.

Tabbas an samu nuna zafin kai tsakanin bangarori guda biyu: Kwankwasiyya da Gandujiyya. Kwankwasiyya suna ganin tunda suna da Madugu kawai an gama, su kuma tsagin Gandujiyya suna ganin ai sune suke da gwamnati sama da kasa. Wannan tunanin yasa kowane bangare yana ganin cinta da ‘dan uwansa saidai a karshe Allah ya tabbatar da shine dahir kuma kotun sa itace karshe.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Babu wani kamar Allah, ko kusa ma ba za a taba samu ba. Shiyasa kowa ya gama zafin kai kuma a karshe ya garzaya kotun Allah saboda dukkaninsu babu wanda ya san mai zai faru idan an tafi zagaye na biyu a zaben da za ayi ranar 23 ga Maris.

A mataki na farko dai, kowa a cikinsu bai yi tsammanin zaben zai kasance yadda ya kasance ba. Misali, idan ka tambayi ‘dan kwankwasiyya kafin zabe zai ce maka zai ci zabe kuma babu wanda ya isa yayi masa magudi tunda yana da madugu. Shima ‘dan gandujiyya zai nuna maka yana da kwarin gwiwa saboda yana da gwamnati a hannu.

Bayan kammala zabe sai kallo ya koma sama, sakamakon zaben yasa sun kare da zagin junansu, a wasu yankunan ma ban da fada da sare-saren juna babu abun da suke. Bayan fitowar sakamako daga hukumar zabe, bayyana zaben a matsayin bai kammala ba (Inconclusive) ta kara kusantar da mabiyan bangarorin guda biyu ga Allah duba da yadda suka dukufa wajen addu’o’in neman nasara daga Allah.

Lallai Allah ya tabbata madaukakin sarki, duk inda bawa ya kai da zafin kai ko girman kai dole za a wayi gari zai gane girman Allah da kasancewarsa mai iko akan komai insha Allah.

Allah ya kaimu zaben lafiya ya kuma zaba mana mafi alheri.

Share.

game da Author