Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, reshen Arewa ta daukacin jihohi 19 da Abuja, ta tayaShugaba Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa da ya yi na ranar 23 Ga Fabrairu.
Cikin wata wasika da kungiyar ta aika wa Buhari mai dauke da ranar 1 Ga Maris, 2019, kungiyar ta ce sake nasarar da ya yi ta tabbatar da gaskiyar sa da kuma yadda ya ke gudanar da aiki ba tare da kumbiya-kumbiya ba.
Shugaban Kungiyar na Arewa, Yakubu Pam ne ya sa wa wasikar hannu tare da yin kira ga Buhari da gaggauta hada kan kasar nan tare da tashi haikan wajen shawo kan matsalolin tsaro da kuma cin hanci da rashawa.
CAN ta kuma yi kira ga Buhari da ya ja kokarta ya ja kowane bangare na
‘yan Najeriya a cikin gwamnatin sa, kamar yadda ya yi alkawari a wannan gwamnati da zai sake kafawa mai zuwa cikin zangon sa biyu.
Ta ce a yanzu ne kasar nan ta fi cancantar Buhari ya tashi tsaye tsayin daka ya hada kan al’ummar cikin ta.
Ita ma Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI ta mika sakon murna ga Buhari da dukkan sauran wadanda suka shiga takara da jama’ar da suka fito suka jefa kuri’a a cikin kwanciyar hankali a kasar nan baki daya.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Abubakar ya tura sakon a cikin wata takarda da Sakataren JNI, Khalid Abbakar ya sa wa hannu, jiya Lahadi, a Kaduna.
Sultan ya ce, “Mu na godiya ga Allah da ya kawo aka yi zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya cikin zaman lafiya, kuma aka bayyana wanda ya samu nasara.
“Sai dai kuma mu na rokon sauran ‘yan takara don Allah su yi hakuri, su maida takubban su a cikin kube, su hakura, domin a kowace irin takara dole sai wani ya yi nasara, wani kuma ya fadi.
Ya ce a wannan takara kowa ma ya yi nasara, domin abu mafi muhimmanci da ake bukata shi ne dorewar zaman zaman lafiya.
Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su hori magoya bayan su su yi riko da zaman lafiya da juna a cikin lumana.
Discussion about this post