Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke belin shugaban kungiyar tawayen IPOB, Nnamdi Kanu.
IPOB kungiya ce ta matasa zalla masu kumajin kafa jamhuriyar Biafra.
Nan take kuma ta bada umarnin cewa jami’an tsaro su kamo Kanu a duk inda suka gan shi.
Mai Shari’a Binta Nyako ce ta bayar da wannan umarni a yau Alhamis, tare da umartar a gaggauta bai wa ‘yan sanda waranti da sammacin iznin kamo Kanu.
Kotu ta ce ta bayar da odar kamo shi ne saboda ya ki ya bayyana a gaban mai shari’a, tun bayan da aka bayar da belin sa a cikin watan Afrilu, 2017.
A yau kotu ta ce tilas a ci gaba da shari’ar sa, tare da umarnin a sake aza wata sabuwar ranar da za a bai wa bangaren gwamnati da na wanda ake kara da lauyoyin sa domin a ci gaba da sauraren karar duk kuwa da cewa Kanu ba ya halartar kotun.
Kanu ya gudu ne bayan da sojoji suka yi wa gidan sa kawanya, inda ya sulale.
Daga baya ya bayyana a kasar Isra’ila, inda ya ci gaba da sukar gwamnatin Muhammadu Buhari.
Discussion about this post