A ranar Laraba ne babbar kotun dake Apo a Abuja ta yanke wa wani boka mai suna Clement Joseph mai shekaru 43 hukuncin daurin shekara 97 a kurkuku bayan ta kama shi da laifin damfarar wani Naira miliyan 5.6.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta kama Joseph wanda aka fi sani da Dr Omale da laifin aikata laifuka bakwai da suka hada da damfarar mutane makudan kudade.
Alkalin kotun Angela Otaluka ta ce ta yanke wa Joseph hukuncin haka ne ba tare da beli ba bisa ga hujjojin da suka tabbatar wa kotun cewa lallai Joseph ya aikata wadannan laifuka.
Otaluka ta bayyana cewa shekaru biyu da Joseph ya yi yana tsare a kurkuku kafin a yanke masa hukunci basu cikin shekaru 97 din da zai yi.
Ta kuma umurci Joseph da ya biya Bola Akinbola matar da ya damfara Naira miliyan 5.6
A karshe Otaluka ta yi watsi da rokon sassaucin da lauyan dake kare Joseph, Johnbull Adara ya nema a madadin Joseph. Ya bayyana cewa wannan shine karon farko da Joseph ya aikata irin wannan laifi sannan kuma gashi yayi zaman shekaru biyu tsare a kurkuku.