Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar mafarki ya ke yi cewa da yayi wai shine ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Kaduna.
” Atiku bai taba yin nasara a zaben shugaban kasa a Kaduna ba. Tun da shugaba Muhammadu Buhari ya fara takara a 2003, zuwa 2015 PDP bata taba yin nasara a zaben shugaban kasa a jihar Kaduna ba. Saboda haka ba yanzu bane za a ce wai Atiku yayi nasara a Kaduna ba.
” Ina so in tabbatar muku cewa ko sau 10 aka yi zaben shugaban kasa a Najeriya, Atiku ba zai taba cin zaben Kaduna ba.
Kuri’un da aka ce wai ya samu a zaben a kaduna ma da bai kai haka ba. Ya samu har 400,000 ne saboda wasu sun yi zabe ba da na’urar tantance kuri’u ba.
” Sannan kuma cewa da yayi wai na’urar adana kuri’un da aka kada na hukumar zabe ne ya bayyana wannan sakamako da ya ke gadara da, zuki ta malle ne domin kowa ma zai iya siyan irin wannan na’ura ya saka mata suna na hukumar zabe sannan ya fadi abin da ya ga dama.
” Amma idan ma haka ne ay zamu hadu a kotu inda zai yi bayanin yadda ya samu wannan kuri’un boge da yake gadara dasu.
El-Rufai ya karyata rade-radin da ak yi ta yadawa wai yayi hatsari ya karya wuya, yanzu rai a hannun Allah. ” Ina nan lafiya kalau sumul, babu abin da ya same ni. Kuma ni dai ban yi hatsari ba. Duk wadannan kulle-kullen makiya ne kawai.”