Ma’aikatan kiwon lafiya a Abuja sun bayyana cewa akwai wani magani da ake kira ‘Post Exposure Prophylaxis (PEP)’ wanda ke da ingancin kare mutum daga kamuwa da cutar Kanjamu.
Malaman asibitin sun bayyana cewa mutum zai iya amfani da wannan maganin ne idan akwai yiwuwar cewa kwayar cutar kanjamau ya shiga jikin mutum.
Kamar yadda aka sani za a iya kamuwa da kanjamau ta hanyar yin jima’I da wanda ke dauke da cutar, yin amfani da reza ko kuma allurar da wanda ke dauke da cutar ya yi amfani da dai sauran su. Amma maganin zai samar wa mutum kariya idan mutum ya juri shan sa na tsawon wata daya kokuma makoni hudu.
” Mutum zai iya fara amfani da wannan maganin ne bayan an yi gwaji an tabbatar cewa baya dauke da cutar kuma idan akwai yiwuwar cewa kwayar cutar ya shiga jikin mutum a cikin awa 72 kokuma kwanaki uku’’.
Za a iya samun wannan maganin ne a asibitocin gwamnati da wadanda ke zaman kansu a kyauta sai dai bincike ya nuna cewa ba duka shagunan siyar da magungunan ba ne ke siyar da wannan magani sannan idan ma an samu zai iya kasancewa da tsada.
Sai dai a wani bincike da wakiliyar PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa ba kowa bane ke da masaniya game da wannan magani ba ballantana ace za a iya samun ta.
Wani mutum mai suna Wasiu mai shekaru 35 ya ce da yana da masaniyar wannan maganin da tuni ya gaggauta zuwa asibiti domin samun wannan magani.
Ita ma Deborah ta koka bisa rashin sanin wannan magani sannan ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya kan wayar da kan mutane game da wannan magani.
RA’AYOYIN MA’AIKATAN FANNIN KIWON LAFIYA GAME DA PEP
Da yake tattaunawa da wakiliyar PREMIUM TIMES ma’aikacin kiwon lafiya Tolu Fakeye ya bayyana cewa kamata ya yi fannin kiwon lafiya ta samar da wadannan magani a duk asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya dake kasar nan.
Adediran Abdulhameed ma’aikacin kiwon lafiya ya ce bai goyan bayan a fara siyar da wannan magani a shagunan siyar da magunguna ba domin gudun amfani da maganin a hanyoyin da bai kamata ba.
” An sarrafa wannan magani ne domin kare wadanda basu dauke da Kanjamau daga kamuwa da cutar sannan siyar da wannan magani da shagunan siyar da magunguna ka iya ingiza mutane yin amfani da wannan magani ba tare da izini likita ba.
Abdulhameed ya kuma kara da cewa bai kamata a barwa gwamnati nauyin wayar da kan mutane game da wannan magani ba ya kamata kowa ne ya mai da hankali ya taya gwamnati siyar da wannan magani.
Discussion about this post