KIWON LAFIYA: Abubuwan da za a kiyaye kafin a sha magani

0

Ga bayanan wasu sharudan da mutane ke yawan karyawa wajen shan magani;

1. Shan magani kafin ko kuma bayan an ci abinci

Wasu magunguna kamar maganin zazzabin cizon sauro, typhoid, maganin cutar siga, maganin kara karfi a jiki na bukata aci abinci kafin a hadiye su domin su yi aiki yadda kamata a jikin mutum.

Rashin kiyaye wannan sharadin na sa a sami matsaloli da dama kamar su ciwon kai, rudewa, jiri da sauran su a maimakon magani ya yi aikin da ya kamata a jikin mutum.

Sannan shan magani kafin a ci abinci kamar su maganin tsutsan ciki, ana shan su ne kafin a ci abinci zuwa bayan anci abinci da dadewa.

2. Wasu ire iren abinci na haka magani yin aiki

Malaman asibiti su bayyana cewa cin ganyan latas,ci abincin dake dauke da sinadarin ‘Vitamin K’ da ‘Grape Fruit’ ga wanda ke fama da cututtukan dake kama zuciya,ko kuma aka yi wa fidan canza wani bangaren jikinsa kamar koda na hana magungunan da suke sha aiki a jikinsu.

Malaman asibiti sun ce kamata ya yi a ci irin wadannan abin cin kadan domin mahimmancin da suke da shi a jikin mutum amma yawan cinsu tare da wadannan magunguna na cutar da mutum.

3. Giya

Malaman asibiti sun bayyana cewa shan giya abu ne dake matukar cutar da mutum kuma shan shi da magani na kowani iri na cutar da kiwon lafiyar mutum.

Hada magani da giya na hana maganin aiki a jikin mutum sannan yin haka na cikin hanyoyin kamuwa da cutar koda, gyambon ciki, daji da makamantan su.

4. Madara

Bai kamata a sha magani ba da madara ba domin madara na hana magungunan kamar su ‘Antibiotics, Tetracycline da Ciprofloxacin’ yin aiki yadda ya kamata. Idan ya zama dole asha madaran, sai a dan bari tukunna har sai bayan awowi da shan maganin.

A karshe malaman asibiti sun yikira ga mutane da su kiyaye sharudan shan magani. Abi yadda aka ce a sha ya fi.

Share.

game da Author