Babban kotu a jihar Kano ta soke takarar dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Abba Yusuf cewa bai cancanta ya yi takara a karkashin jam’iyyar ba.
Alkalin kotun da ya yanke wannan hukunci Lewis Allagoa ya ce ya jam’iyyar PDP bata yi zaben fidda gwani ba, nada Abba ta yi. A dalilin haka kuwa ta soke takarar sa.
Idan ba a manta ba anyi ta kai ruwa rana a jam’iyyar PDP tun bayan canja sheka da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya yi daga APC zuwa PDP.
Wasu da dama sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda jam’iyyar ta ke gudanar da al’amurorin ta da kuma yadda aka fidda dan takarar gwamnan jihar a wancan lokaci.
Al’amin Little wanda shima ya yi takarar kujerar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar PDP din shine ya garzaya kotu domin a rusa wannan zabe na Abba Yusuf da jam’iyyar ta yi.