Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya caccaki Buhari dangane da kiyasin kasafin kudin 2019 da ma na can shekarun baya da ya gabatar a Majalisa.
Dogara ya yi wannan kakkausar suka ce a gaban jama’a yayin da ya ke jawabin bude taron fara saurare da bin kadin abin da kasafin na 2019 ya kunsa.
Kakakin wanda dan PDP ne, jam’iyyar Adawa, ya ce dukkan kasafin kudaden da Buhari ke kai wa Majalisa, ana tsara su ne kawai domin biyan bukatar masu tsara kasafin kawai.
Ya ce kasafin kudaden a koda yaushe su kan karkace daga turbar da al’ummar kasar nan za ta fi amfana da su.
Daga nan kuma sai ya soki lamirin yadda ministoci suka gabatar wa Majalisa da na su kasafin kudaden a makare.
“Irin yadda ma’aikatu ke zabar ayyukan da za su yi, ya kan kauce daga ainihinn abin da ya kamata, tare haifar da matsala wajen aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin.
“Don haka idan ba a kawar da wannan gagarimar matsala ba, to a haka za mu yi ta tafiya, kowace shekara ba za a iya aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin shekarar ba.”
Dogara ya kara da cewa su mahukuntan gwamnati da ma’aikatu sun fi karkata ne a inda suke so a kashe kudaden kasafi, ba inda ya kamata ko ya fi cancanta a kashe kudaden, ko a yi ayyukan ba.
Ya kuma nuna takaicin yadda a shekara ba a iya aiwatar da ko da fiye da rabin kasafin kudin shekara.
Dogara ya kuma wanke Majalisa daga laifin da wasu ciki kuwa har da jami’an gwamnati ke dora mata cewa ita ke kawo tsaikon rashin gudanar da ayyukan da ke kunshe a cikin kasafin kudi.