Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuhu!
‘Yan uwana masu girma! A yau laraba, mun wayi gari da wata shedaniyar makala ta sharri, wadda azzaluman ‘yan siyasa da ‘yan koren su da magabta, makirai suka rubuta, suka tsara don su bata sunan Adilin Sarki, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu. Wannan rubutu yana nan yana yawo a kafafen yada labarai na zamani, wato Facebook, WhatsApp da sauransu. Taken wannan makala shine kamar haka:
“ASIRI YA TONU, SARKIN KANO YA TAIMAKI PDP A ZABEN GWAMNAN KANO, YA KUMA SHIRYA ZANGA-ZANGA A BOYE AN JE FADARSA.”
A cikin wannan shedaniyar makala ta sharri, da Allah, wanda baya bari ayi zalunci, ya tona asirin su, wai suke cewa:
“Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yasha alwashin karya gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta hanyar marawa jamiyyar PDP baya a zaben nan da aka yi da kuma karashen zaben da za’a yi nan gaba. An samu labari mai tushe tabbatacce cewar Sarki Sanusi ya rantse da Allah cewar tun wancan lokacin da gwamnatin jihar Kano ta kautar da kai wajen binciken da majalisar dokokin jihar Kano takewa Sarkin kan wata badakala da ake zargi a fadar masaurautar Kano, shi Sarki Sanusi ya dau alwashin sai ya tozarta gwamna Ganduje. A wata tattaunawa ta sirri da Sarkin na Kano yayi da Kwankwaso da Obasanjo kwanaki kadan kafin zaben gwamnan a garin Otta, can gidan Obasanjo, Sarkin Kano ya dau alwashin sai yaga bayan Gandujen a wannan zaben. Haka nan majiya mai tushe ta kara tabbatar da cewa kwana daya kafin zaben gwamnan, Sarki Sanusi ya tara manyan mutane dake zaune a cikin gidan masarautar Kano ya nuna tilas ne gare su dasu zabi PDP. A nan kuma rikici ya barke tsakanin magoya bayan tsohon Sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, in da wani dattijo ya mike tsaye ya zagi Sarkin a gaban kowa, cewar bai isa ya gaya musu wa zasu zaba ba a zaben gwamna. Tsohon yace haka nan a zaben shugaban kasa Sarkin yace musu su zabi Atiku Abubakar wai shugaba Buhari ba shi da kyakkyawar kwarewar rike kasa, ba shi da ilimin tafiyar da tattalin arzikin kasa. A nan ne fa aka fara samun tirjiya daga mutanen da Sarkin yasa a tara yayi musu hudubar zaben PDP. Haka nan a gaban kowa ne Danmajen Kano, wanda kani yake ga Sarki Sanusin, bayan yayi nasa zaben na gwamna ya daga ya nunawa jama’a zaben da yayi wa PDP saboda kowa ya tabbatar. Daga cikin dabarun da Sarkin Kano din ya gayawa yan PDP din shine, wai su shirya wata zanga-zanga su kewaya gari da sunan wai suna neman hukumar zabe ta gaggauta sanar da PDP sun ci zabe, idan kuma ba haka ba wai zasu tayar da zaune tsaye a jihar Kano. A halin da ake ciki yanzu ‘yan PDP din sun yi wannan zanga zanga kuma sun je fadar Sarkin. An kuma kara tabbatar da cewa Sarkin Kanon ya kara tabbatarwa da jama’ar cewa matsawar yana kan karagar masarautar Kano, sai ya tunbuke gwamna Ganduje a kan karagar mulkin Kano. Jama’a ayi hattara. Masarautar Kano ta zama masarautar tayar da hankalin jama’ar Kano maimakon kwantar da hankalin jama’a. Allah Yayi mana maganin duk wani mai son haifarwa Kano da tashin hankali, amin. Zaman lafiyar mu kawai shine jam’iyyar Baba Buhari, wato APC.”
Ya ku Jama’a! Wannan fa shine sharri da kage, da yarfe da wasu miyagun ‘yan siyasa da yaran su, suka tsara, suna yada wa, domin bata suna da cin mutuncin wannan shugaba mai daraja, mai tausayin talakawansa, wato Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu!
Haba Jama’a! Wannan ai ko shugaban jahilai ba zai yarda da wannan karyar ba wallahi. Domin Mai Martaba Sarkin Kano mutum ne mai yafiya, mai kau da kai daga abubuwan da suka gabata, mai yarda da kaddarar Allah. Sannan wallahi, shi mutum ne marar riko, ba ya rike kowa da wata manufa, ko wani abu da ya faru a baya!
Kuma ina mai rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, wannan maganar karya ce, kage ne, kuma sharri ne! Kuma na rantse da Allah, Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ba zai yi wannan ba! Kawai magabta ne da makiyan mai Martaba suke yada wannan. Kuma da yardar Allah, abun da suke nufi na batanci da zubar da mutuncin mai Martaba, Allah ba zai basu nasara ba! Domin Allah ba azzalumi ba ne!!
Kawai don talakawan Kano sun ce basu yarda ba, a basu abunda suka zaba, basu yarda ayi masu murdiya ba, shi kenan sai kuke neman ku huce fushin ku akan wannan bawan Allah?
Haka zaluncin naku zai koma kan shuwagabannin addinin mu? Ba ku san masarautun mu suna wakiltar addinin mu bane na Musulunci? Ba ku san cewa taba su taba addinin mu bane? Me yake damun ku ne? Kada fa ku jawo wa kan ku matsalar da baku iya tarewa fa! Ina mai baku shawara, wallahi, ku tsaya kan siyasar ku. Kada kuce za ku shigo cikin farfajiyar addininmu da mutuncin mu! Domin wallahi, taba masarautun mu taba addinin mu ne. Saboda haka kuyi hankali. Wallahi bakin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne! Idan ba rashin kunya ba, ina ruwan Sarkin Kano da siyasar ku? Wane irin shakiyanci ne wannan?
Ya ku Jama’ar jihar Kano! Ya ku Jama’ar Najeriya!! Ina mai kira a gare ku, da ku manta da wannan shirme da ake yada wa, da zimmar cin mutuncin wannan bawan Allah, wato Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II.
Wannan sharri ne, zalunci ne, munafunci ne, aiki ne na miyagu, magabta, wadanda basu son cigaban jihar Kano da talakawan ta. Suna so ne kawai su dauke hankulan Jama’a daga ainihin abunda yake faruwa. Kuma da karfin Allah ba zasu ci nasara ba.
Ya ku Jama’a! Ku sani, wallahi taba Sarakunan mu, taba addinin mu ne, cin mutuncin su, cin mutuncin addinin mu na Musulunci ne! Zubar da kimar su, zubar da kimar addinin Musulunci ne. Don haka mu kiyaye, kuma kar mu yarda da wannan sharri. Sarakunan mu masu mutunci ne, masu son talakawa ne, kuma mutane ne masu kaunar zaman lafiya da cigaban talakawan su.
Ya Allah ina rokon ka! Duk wanda yake neman murkushe abokin adawarsa ta siyasa ta hanyar magudi da zalunci, karya da sharri, Ya Allah ka hana masa jin dadin mulkin ko wanene shi!
Ya Allah! Ka tarwatsa gwamnatinsa a boye da bayyane.
Sannan muna nan muna ta addu’a da fatan alheri a koda yaushe ga ‘yan siyasa masu son talakawa kuma masu gaskiya.
Allah yasa mu dace, amin.
Dan uwanku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto wannan sako daga Okene, jihar Kogi, Nigeria. Zaku iya samun sa a: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.