Idan ba a manta ba Kakakin Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu ya bayyana wa manema labarai cikin takarda da ya fitar da yammacin Juma’a daga hedikwatar jam’iyyar APC cewa jam’iyyar ta dakatar da gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun da gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha daga jam’iyyar.
Duk da cewa jam’iyyar APC din ta dakatar wadannan gwamnoni, ta mika takardar neman a kore su kwata-kwata daga jam’iyyar ga kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Idan dai ba a manta ba, da Amosun da Okorocha duk suna mara ma wata jam’iyya ce baya a zaben gwamna mai zuwa ba APC ba.
Jam’iyyar bata dauka wannan hukunci ba sai bayan da ta lashe zaben shugaban kasa.
Ana haka ne kuma jam’iyyar ta sake fidda wani sanarwar na dakatar da ministan Neja-Delta Pastor Usani Usani da Shugaban Muryar Najeriya VON, Osita Izunaso.
Dukkan su an same su da laifin yi wa jam’iyyar zagon kasa, inda suke yi wa jam’iyyar fuska mai fara’a amma na ciki na ciki.
Lanre ya ce suma an mika sunayen su ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar domin tabbatar da korarsu kwata-kwata daga jam’iyyar.
Discussion about this post