Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna na jihar Kano.
Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe ne, Bello Shehu ya bayyana haka a yau Litinin.
Hakan ya biyo bayan hargitsa cibiyar tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Nassarawa da ita kadai ta rage, da aka yi cikin daren jiya Lahadi.
“Yayin da mu ke komawa mu ci gaba da tattara sakamako, sai muka samu labara maras dadi cewa an je Karamar Hukumar Nassarawa inda ake tattara sakamakon karamar hukumar, an hargisa wurin kuma an kekketa takardun da ke dauke da sakamakon zaben da suka gudana a rumfuna da mazabu.
“A zaman yanzu dai babu wancan sakamakon zabe a hannun mu. Domin ma sai da ‘yan sanda suka kubutar da wasu mutane a wurin.
“ Amma niyyar mu ita ce mu koma mu bi daki-dakin sakamakon da ke cikin na’urar tattara bayanan kuri’un da aka tara daga rumfuna da kowace mazaba.
Ya ce idan suka yin haka ne za su bayyana sakamakon da doka ta amince a karba, da wanda doka ba ta amince a karba ba.
Jami’in tattara bayanai na jihar Kano, Farfesa Shehu ya ce ma’akatan san a duba kuri’un da aka soke, wadanda y ace sun a da yawa.
Daga nan ya ce za su tantance a cikin kuri’in su gano yadda za a samu karancin su.
Ya ce ta haka ne za a iya gano wanda ya yi nasara.
Shi kuma Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, na Jihar Kano, yace a inda suka gano cewa akwai ko an yi zabe ba da ‘card reader’ ba, to sifili za a bayar a kawai a wuce wurin, a ci gaba da aiki.