Kamuwa da cutar ‘Syphilis’ ga mai ciki na cutar da dan dake cikin ta – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mata masu ciki da su kiyaye kan su daga kamuwa da cutar ‘Syphilis’ domin guje wa haiho nakasassun jarirai.

Cutar ‘Syphilis’ cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar jima’I da amfani da bandakin da bashi da tsafta.

WHO ta yi wannan kira ne ganin cewa cutar na daya daga cikin cututtukan dake yawan kawo barin ciki ga mata da kisan jarirai da zarar an haife su.

A yanzu haka mata 661,000 na dauke da wannan cutar inda a dalilin haka mata ke yawan samun bari,haifo bakwaini da sauran su.

Jariran da suka kamu da wannan cuta daga iyayen su mata kan yi fama da matsalolin rashin girman jiki,rashin kasusuwa masu karfi,fatar jaririn zai rika zagwanyewa,kunburarren huhu,kamuwa da cutar ‘Jundice’ da sauran su.

Bincike ya nuna cewa rashin samun maganin wannan cutar ga mai cikin dake dauke da cutar ne ke haifar da wadannan matsaloli ga jarirai.

WHO ta ce mata za su iya gujewa haka ne idan suna zuwa awo a asibiti da zarar sun dauki ciki, amfani da kororo roba domin guje wa kamuwa da cutar a lokacin yin jima’I sannan a gujewa amfani da bandakin da bashi da tsafta.

Share.

game da Author