KAJURU: An kashe mutane 16 a harin Kajuru –‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da harin da aka kai wa kauyen Unguwar Barde dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna cewa an rasa rayuka 16.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yakubu Sabo ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kaduna.

Ya ce maharan sun far wa kauyen ne da karfe 7:30 na safiyar Lahadi.

” Mu kuma da jin haka tare da sojoji muka gaggauta zuwa kauyen domin dakatar da hakan.

” A yanzu dai zaman lafiya ya fara dawowa kauyen.

Sabo yace kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Abdurrahman ya yi wa mutanen kauyen ta’aziyar mutanen da suka rasa sannan ya lashi takobin ganin cewa rundunar ta kamo duk wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wata majiyya ta tabbatar cewa wasu mahara sun kai wa wasu kauyuka biyu hari a karamar hukumar Kajuru jihar Kaduna.

Wadannan kauyuka kuwa sun hada da kauyen Kirimi da Iri, Dogon Noma.

Wani mazaunin yankin mai suna Hon. Stingo ya bayyana cewa maharan sun far wa kauyen su ne da misalin karfe bakwai na safe.

” A safiyan yau ne karan tashin harsashi ya ruda kowa a kauyen nan a dalilin harin da wadannan maharani suka kawo mana.

” Maharan sun kasa kansu kashi uku inda kaso na farko suka shigo suna harbin mutane, kaso na biyu kuwa suka fara kona gidajen mutane sannan kaso na uku suka harbe wadanda suka shiga daji domin tsirar da ransu.

Har yanzu dai babu tabbacin ko su wanenen wadannan mahara da suka far wa kauyukan Kajuru.

Share.

game da Author