KADUNA: Buhari zai sake zuwa Kaduna don yi wa El-Rufai Kamfen

0

Akwai yiwuwar shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sake zuwa garin Kaduna kafin wa’adin kamfen din gwamna ya cika wato awa 24 kafin zabe, domin sake yin kira ga mutanen Kaduna su zabi gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan APC a jihar Kaduna suka tsokata wa wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA a garin Kaduna.

Akwai yiwuwar reshe zai iya juyewa da mujiya muddun ba shugaba Buhari bane ya sake zuwa garin Kaduna domin rokon jama’a da su maida wukakensu su sake ba gwamnan jihar Nasir El-Rufai dama a karo ta biyu domin karisa ayyukan da ya faro.

Duk lungun da ka shiga a garin Kaduna, za ka ji mutane gungu-gungu suna tofa albarkacin bakin su game da zaben gwamna dake tafe.

Yanzu dai abin ya canja salo, domin kuwa kusan abin ya koma siyasar addini da kabilanci.

Malaman addinai sun koma sai kira suke yi ga mabiyansu dasu zabi dan takara wane ko kuma jam’iyya kaza.

Kowa dai a cike yake yana jiran Allah ya kaimu ranar Asabar ya zabi wanda ya ke so.

Ga dukkan alamu cikin gwamnati mai ci ya duri ruwa domin bayan bakin adawa da mutanen yankin Kaduna ta kudu ke yi wa gwamnatin, a yankin Kaduna ta tsakiya da ta Arewa ma akwai aiki matuka a gaban ta.

Bayan da cewa shi kansa dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP Isah Ashiru dan asalin yankin ne, wato yankin Zaria domin ma basarake ne sannan kuma duk jiga-jigan ‘yan jam’iyyar sa ta PDP duk ‘yan yankin ne, sannan akwai matsalar rashin gamsuwa da mutanen yankin suke yi wa wannan gwamnati.

Baya ga matsalolin da aka yi ta fama da su wajen sallamar ma’aikata da wasunsu ba a biya su kudin sallama ba, akwai kuma gani da ake yi na cewa shi fa wannan gwamna mai ci ba mutum bane mai yin nadama.

Sai dai kuma duk da hakan da a ke tottofawa game da gwamnan jihar, da dama kuma na ganin shine yafi dacewa da mulkin jihar Kaduna.

” Jihar Kaduna na bukatar jarumi irin Nasir El-Rufai, wanda ba za a iya juya shi ba. Ana bukatan gwamna mai dattaku da sanin ya kamata. Wanda idan ya sa gaba sai ya cimma burin sa.” Haka Sani Audu wani mazaunin Kaduna ya fadi.

Sannan kuma ga ambaliyar canja sheka da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka yi zuwa APC. Hakan duk hanyoyi ne da zai ba jam’iyyar daman iya lashe zabe a jihar.

Yanzu dai dubara ya rage wa mai shiga rijiya. Amma fa ga dukkan alamu za a gwabza a zaben ranar 9 ga watan Maris.

Share.

game da Author