Duk da cewa akwai babutuwa ko matsalolin da suka taru suka yi wa Gareth Bale katutu a cikin watannin da suka shude a ci gaba da wasan sa cikin kungiyar Real Madrid, amma babban abin da ya fi haifar masa da zaman kadaici shi ne rashin nuna sha’awar da ya yi na koyon harshen Sipananci da ake amfani da shi a kasar Spain.
Bale, wanda dan kasar Wales ne, kasar da ke karkashin rukunin kasashen da suka kunshi Birtaniya, Turancin Ingilishi ya ke ji, babu ruwan sa da Sipananci.
Shekarar sa ta shida kenan a kungiyar Real Madrid, amma har yau ko ‘zo in kashe ka’ bai iya da harshen Sipananci ba.
An yi wani dan wasan kasar Ireland mai suna John Aldridge wanda ya dan yi zamani kadan a kungiyar Real Sociedad ta kasar Spain. Da ya ke shi ma Turancin Ingilishi ya ke yi, ba Sipanci ya ke ji ba, an shawarce shi cewa idan ya na so ya ji dadin zama kada a raina shi, to ya hardace kalmoni uku kawai, sun ishe shi zaman Spain.
“Hijo de puta” su ne kalmomin da aka ba shi shawara ya iya. Ma’anar kalmonin itac e ‘shege dan karuwa!’
Shekaru kusan 30 kenan da Aldridge ya yi zamani a Spain, amma har yau kasar ba ta canja wa Turawan Birtaniya masu zuwa kasar wasa ba.
Akwai raini, ko kuma kallon-kallo tsakanin Turawan Birtaniya da na Spain. Su dai na Birtaniya na Gadara da kuma tinkahon cewa sun fi na Spain wayewa a duniya. Su kuma Turawan Spain na tinkaho da bugun kirjin cewa duk iya kwallon ka to ba za ka shahara a duniya ba, sai ka zo Spain ka yi wasa, sannan za ka zama wata tsiya.
Tsawon shekaru shida da Bale ya shafe a Madrid, har yau har kwanan gobe ya ki tsayawa ya koyi harshen Sipancin da zai rika ko da mu’amala ce da ‘yan wasa, musamman a cikin dakin da ake canja kaya da kuma hutawa a lokacin wasanni.
Wata matsalar da ke damun Gareth Bale kuma ita ce yadda tauraruwar sa ta dan disashe, tun bayan nasarar da Madrid ta samu a kan Liverpool FC, a wasan karshen na cin Kofin Zakarun Turai, inda Bale ya jefa kwallaye biyu shi kadai a ranar.
Tun da aka shiga sabuwar kakar wasanni, Gareth Bale sai kara maida kan sa na-ware-ga-dangi ya ke ci gaba da yi.
Wadanda ke da kusanci da shi sun tabbatar da cewa sai kara ware kan sa ya ke ci gaba da yi daga cikin auran ‘yan wasa. Dama kuma ba ya jin yaren na Sipananci ballantana ma ya rika hira ko raha da wasu.
Akwai wata al’ada ta kasar Spain, wadda ake shirya dina tun 11 na dare har sai gari ya waye ana dabdala. To Gareth Bale da Toni Kroos babu ruwan su da irin wannan dabdalar.
Matsawar lokacin barcin Bale ya yi, to ba ka da wanda ya isa ya hana shi tafiya ya kwanta barci. Kuma idan safiya ta yi, ba za ka taba ganin ya yi lattin zuwa filin tirenin ba. Haka sabon dan wasan Madrid Courtous Thibaous ya bayyana.
Marcelo kan sa ya damu kwarai da yadda ba ya iya yin hirar komai da Gareth Bale.
Marcelo ya ce tun bayan da Cassilla ya bar Madrid, a yanzu ya na zaunawa ne kusa da Gareth Bale a cikin dakin da ‘yan wasa ke hutawa.
“Na yi iyar kokari na don mu rika hira da Bale. Amma bai san komai ba, shi ya sa kalmomi uku kadai ku ke yin magana da su, wadanda su ne ya iya kadai.
“Daga ‘sannu’ sai ‘barka dai’ sai kuma ‘sai an jima’.”
Bale ya shiga damuwa tun bayan da Madrid ta sayo sabon yaron hatsabibin dan wasa, Vinicius Junior, dan kasar Brazil. Tun da yaron ya je Madrid, Bale bai kara yin wasa har aka gama ba a cire shi ba. Sau da dama sai an kusa tashi ma ake sako shi. Sau biyu aka fara wasa tare da shi.
Ba Gareth Bale ne kadai ke da irin wannan dabi’ar ba. Haka ta faru da David Platt da Gary Lineker na can shekarun baya, da kuma Jadon Sancho a yanzu. ‘Yan wasan Birtaniya ba su cika maida hankali wajen koyon yaren wata kasar da suka fita suke wasan kwallo a can ba. Wannan kuwa kan haifar musu da gagarimar matsalar da har salon takun wasan su ta kan shafa.
Duk da haka dai Bale ya nuna cewa shi dan wasa ne da duniya ke tutiya da shi. domin dukkan kofin Champions Legue hudu da Madrid ta ci a daga zuwan sa, duk da gagarimar gudummawar sa aka samu nasarar.
Amma kuma ga yadda lamarin ke tafiya a yanzu, idan Bale ya kammala wannan kakar a Madrid, ban ga dalilin ci gaba da zaman sa a Spain ba. Ya rigaya y agama cin rabon sa a kasar. Me kuma zai zauna ya yi?
Discussion about this post