JOS: Yadda aka yi garkuwa da wakilin PREMIUM TIMES don ya dauki hoton kananan yara na zabe a rumfar zaben gwamna

0

A yau Asabar ne aka sace wakilin PREMIUM TIMES mai suna Kunle Sanni, aka gudu da shi saboda ya dauki hoton kananan yara su na bin layin dangwala kuri’a a Rumfar Zaben Gwamna Solomon Lalong na Jihar Filato.

Wasu ‘yan daba ne suka sace shi suka gudu da shi a cikin jeji bayan da suka ga ya dauki hotunan kananan yara masu yawa, wadanda suka shiga layin jefa kuri’a.

Dukkan wadanda suka sace shi din su na yi wa jam’iyyar APC aiki ne a mazabar ta Gwamna Lalong na jam’iyyar APC.

Sanni ya samu nasarar daukar hotunan kananan yaran kowane dauke da katin shaidar rajista.

Kafin ya bar wurin, tuni wani ejan na jam’iyyar APC ya sa ‘yan takife suka kewaye shi, suka hana shi fita daga wurin.

An kwashe sa’o’i da dama ana kakuduba da cukumurda, inda a wannan tsawon lokaci Kamfanin Jaridar PREMIUM TIMES ta tuntubi dukkan wadanda suka kamata, tare da sanar da su cewa kada a sake wani ya taba lafiyar Sanni.

Bayan ya fito daga wajen ashe kuma wasu sun yi masa kwanton-bauna, inda suka yi cacukui da shi suka jefa cikin wata taxi, suka arce cikin jeji tare da shi.

A cikin jejin ne suka tilasta masa lallai ya goge hotunan da ya dauka.

Sanni ya bayyana wa jaridar sa, PREMIUM TIMES cewa rikicin ya tirnike ne a Rumfar Zabe ta PU15, Mazaba ta 04 da ke Karamar Hukumar Shendam, cikin Jihar Filato.

“ Bayan da suka kula da cewa na dauki hotuna, na zo ficewa daga wurin sai wasu ejan na APC suka bi ni suka damke ni. Suka jefa ni mota tare da tilasta ni na goge hotunan.

“Da farko sun bi ni da lalama, domin har kudi naira 20,000.00 suka dauko, suka ba ni, amma na ce zan karba ba.

“ Sun karbi waya ta a lokacin ko caji ma ba ta da shi. Amma suka jona mata caji, domin su ga inda na tura hotunan. Lokacin da suka gamsu cewa na goge hotunan, sai suka ba ni kudi.

“Da farko na ki karba, amma gudun kada su yi min lahani, sai na yanke shawarar karbar kudin na su.” Inji Sanni.

Sanni ya ce dukkan abin da ya faru da farko, ya faru ne a gaban Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Filato, Paul Jatau, da kuma jami’an ‘yan sanda, amma ba su yi komai ba.

Ya ce sai ma Jatau din ne ke shawartar sa da ya goge hotunan mana.

PREMIUM TIMES ta buga daya daga cikin hotun kananan yaran, wanda ya janyo aka sace Sanni.

Share.

game da Author