Kwamishinan Zaben Jihar Kogi, James Apam, ya nuna matukar damuwa da takaicin yadda rikice-rikice suka yi kamari a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a jihar Kogi.
Musamman ya damu da yadda rikicin ya yi muni a mazabar sanata na Kogi ta Gabas.
Ya yi wannan bayani ne a wurin taron masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda zaben shugaban kasa ya gudana a ranar 23 Ga Fabrairu.
Taron kuma ya tattauna yadda za a gudanar da zaben majalisar Jihohi da na dan majalisar tarayya na Kananan Hukumomin Dekina/Bassa.
James ya ce rikicin zabe ya ci rayukan mutane har uku kuma ya hargitsa zabe a rumfuna 157 a Shiyyar Sanatan.
Ya ce rumfuna 89 aka hargitsa a Kananan Hukumomin Dekina da Bassa kadai.
Ya ce an tare mota guda dauke da kayan zabe aka banka mata wuta, ta’asar da ya ce ‘yan daba ne suka aikata a Dekina.
A Karamar Hukumnar Ogori-Magongo kuwa, an kacalcala rumfunan zabe takwas tare ‘card reader’ da kayan zabe.
Daga nan sai Akpan ya jinjina wa masu ruwa da tsaki da suka jajirce a yanzu suka ce a kauce wa fitina a lokacin zabe mai zuwa.
Ya tabbatar da cewa duk wata rumfar zaben da aka yi wala-wala da card reader, to za a soke kuri’un kai tsaye kawai.
Ya ce za a fara rarraba kayan zabe tun a yau Alhamis.
INEC ba za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi ba, sai cikin 2020, saboda a cikin 2015 aka yi zaben gwamnan jihar na baya-bayan nan, ba cikin 2015 ba.
Discussion about this post