Jam’iyyu Tara kadai ne ke da wakilci a Majalisar Tarayya

0

Duk da cewa an bayar da damar kafa jam’iyyun siyasa masu yawa, wannan bai sa yawancin su sun tabuka komai a zaben shugaban kasa, na Majalisar Dattawa da na Wakilai ba.

An yi wa sabbin jam’iyyu har kusan 91 masu rajista a zaben 2019, jam’iyyu 9 ne kadai za su samar da wakilai a Majalisar Tarayya,
INEC ta fitar da sunayen zababbun ‘yan majalisar tarayya. Sai dai kuma akwai kujerun majalisar tarayya 20 da har yau ba a bayyana ba, saboda rashin kammaluwar zaben su.

Daga cikin kujerar wakilai 360, jam’iyyar APC na da 211, sai PDP mai guda 111.

Sauran jam’iyyu da za su samar da mambobin majalisar tarayya sun hada da APGA, guda shida. ADC uku, AA guda biyu sai PRP ita ma biyu.
ADP, APM da kuma SDP kowace na da wakili daya.

Akwai mata 10 daga cikin wadannan 300 da aka sanar da nasarar su.

Share.

game da Author