A wata sanarwa da ta fito daga Darektan Kamfen din gwamna na jam’iyyar PDP, na jihar Kaduna, Yakubu Lere, ta zargi gwamnan jihar Nasir El-Rufai da rabawa wa malaman Kaduna miliyoyin naira domin su yi masa Kamfen.
Wannan sanarwa da ta fito ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamna El-Rufai ya raba wadannan kudade ne ta ofishin hukumar da ke hula da harkokin addinai na jihar, wanda Darektan hukumar, Namadi Musa ya saka wa hannu.
PDP ta yi kira ga hukumar EFCC da jami’an tsaron kasa da su bi diddigin wannan zargi domin akwai kamshin gaskiya a ciki.
Sai dai kuma Darekta Namadi Musa, ya karyata wannan zargi inda ya ce bai taba saka hannu a takarda kamar haka.
” Wannan karya ne saboda signature da aka yi amfani da shi ba nawa bane. Nawa yana karewa da Mohammad ne ba Musa ba. Sannan kuma a matsayin mu na ma’aikatan gwamnati, idan za muyi memo mukan yi a takardar gwamnati ne wanda akwai tambarin jihar kadun a jiki.
” Sannan a ciki akwai wasu ma’aikatan gwamna wato Almisiri da Albani da babu dalilin da za a bani kudi in basu. Saboda haka Ina kira ga Sheikh Tukur Almannar, Sheikh Murtala Shanono, Sheikh Aminu Kuwait, Sheikh Saidu Abubakar, Sheikh Balau da Sheikh Kabiru Gombe daaka nemi a hada ni dasu cewa an bani kudi ban basu ba. Ina rokon su da su yi hakuri da suyafe min.”
Haka kuma a takarda da kakakin gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ya bayyana cewa wannan ruwa ne ya kare wa dan kada.
” Faduwa ce ta tunkaro jam’iyyar PDP da mararatan sun gani a kwanon su cewa mutanen Kaduna ba za suyi su ba a dalilin haka suka rika kirkiro ire-iren wadannan zarge-zarge domin bata alakar mutane da gwamnatin El-Rufai.
” Wannan ba zai dada mu da kasa ba ko kadan domin nasara na tare da mu ne, a jam’iyyar APC. Mutanen jihar Kaduna sun lashi takobin ganin sai sun yi watsa-watsa da PDP a zaben gwamna da za ayi saboda rashin cancantar sa ma tukunna da wasu mishkiloli na dantakarar da suka bayyana karara.
Discussion about this post